✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Kwastam ta kwace shinkafa da kayan N79m a Katsina

Kwastam ta kwace buhu 650 na shinkafa da motoci da man fetur a wata guda Katsina

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kwace kayan abinci da sauran kayayyaki na Naira miliyan 79.3 a cikin watan Agustan 2022.

Kwanturolan hukumar mai kula da shiyyar Katsina, Wada Chedi, ya ce sun kwace kayan abincin Naira miliyan 43.3 da motocin Naira miliyan 35.9 da aka yi fasakwaurinsu zuwa Najeriya daga kasashen waje.

“Jimillar kimar haramtattun kayan da muka kwace ya kai Naira miliyan N79.3 kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike a kansu,” in ji Chedi.

Ya ce kayan abincin da suka kwace sun hada da buhu 594 na shinkafa mai cin kilogram 50 da kudinsu ya kai miliyan N17.6; sai buhu mai kilogram 25 guda 56 da kudinsu ya kama N831,600.

Akwai kuma kwali 96 na makaronin  kasar waje da kudinsa ya kai N576,000; da motoci biyu; man fetur na miliyan 2.2; kwancen tayoyi da dai sauransu.