✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam za ta binciki masu jiragen alfarma

Hukumar Kwastam na zargin manyan mutane da kin biyan haraji.

Hukumar Kwastam ta Najeriya, ta ce za ta fara sabon bincike kan masu jiragen alfarma masu zaman kansu don sabunta takardunsu.

Sanarwa da mai magana da yawun Hukumar, Joseph Attah, ya fitar ta a ranar Litinin a Abuja ta ce tantancewar da za a yi jiragen zai kasance bisa cikakken bin dokokin Najeriya.

  1. IPOB: Gwamnonin Arewa sun yi tir da kisan Gulak
  2. Yadda aka kashe hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

“Saboda kin biyan kudaden haraji da wasu manyan mutane a kasar nan suke yi, Hukumar Kwastam za ta tantance jiragen sama na alfarma da ke kasar.

“Za kuma ta tsaurara wurin bincike da tantancewar domin gano ko an bi ka’ida wajen shigo da jiragen cikin Najeriya.

“Saboda haka, bisa tanadin sassan doka…, Hukuamr Kwastam na gayyatar duk masu jiragen alfarma na zaman kansu da su gabatar da kansu da domin tantance takardu izinin shigo da jiragen,” inji Attah.

Har wa yau, ya kuma bukaci masu kamfanonin jiragen fasinja masu zaman kansu ko wakilansu da su gabatar da rahotannin kamfanonin rahoto ga Hedikwatar Hukumar da ke Abuja.

Takardun da ake bukata su gabatar da takardar shaidar rajista, shaidar gudanar da jirgin sama ta NCAA (FOCC) shaidar kula ta NCAA (MCC), Lasisin NCAA na jirgin sama da ba na kasuwanci ba (PNCF), da kuma shaidar izinin shigo da jirgi ta (TIP).