✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya kara aure

Babu dai cikakkun bayanai kan auren, in ban da wadanda Ali Nuhu ya wallafa a Instagram

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da Kano Pillars, Ahmed Musa ya kara aure, inda ya angwance da amryarsa mai suna Maryam.

Babu dai cikakkun bayanai kan bikin auren, amma wani na kusa da dan wasan kuma fitaccen jarumi a masana’antar fim ta Kannywood, Ali Nuhu ya wallafa hotunan auren a shafinsa na Instagram, inda ya taya sabon angon murna.

Ali Nuhu ya ce, “Ina muku fatan alheri a wannan sabuwar rayuwar da za ku shiga tare, Ahmed Musa ina taya ka murnar kara aure.”

Ahmed Musa da amaryarsa
Ahmed Musa da amaryarsa

A makon jiya ne dan wasan ya yi murnar cikarsa shekara hudu da auren matarsa Juliet, ’yar asalin Ogoja ce a Jihar Kuros Riba.

Kafin ya auri Juliet, Ahmed Musa ya saki matarsa ta farko Jamila, wacce suka haifi ’ya’ya biyu tare da ita.