✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Labarin sace ‘yan sanda 10 ba gaskiya ba ne —Rundunar ’yan sanda

An rawaito cewar ’yan bindiga sun yi awon gaba da ’yan sandan 10.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, Edward Egbuka, ya karyata labarin da ake yadawa cewa an sace ’yan sanda 10 yayin da suke dawowa daga a aikin samar da tsaro a zaben Gwamnan Jihar Osun.

Da yake karyata labarin  a ranar Laraba, ya bayayana ’yan bindiga sun kai wa ayarin ’yan sandan hari ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, amma ba su yi garkuwa da su ba kamar yadda ake yadawa.

Kwamishinan ya kara da cewa a lokacin da aka kai wa ’yan sandan hari, dukkansu sun tsere cikin daji domin gudun kada a yi garkuwa da su.

Egbuka ya ce a lokacin da kura ta lafa, dukkan jami’an su 10 da ake zargin an yi garkuwa da su sun dawo cikin koshin lafiya daga maboyarsu, inda a karshe suka koma tare da abokan aikinsu jihar Nasarawa.

A ranar Lahadi ce Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta bayar da rahoton cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan sanda 10 a hanyarsu ta dawowa daga aikin zaben gwaman Osun da aka kammala a satin da ya wuce.

Wata majiyar ’yan sanda ta ce lamarin ya faru ne a Obajana, a Jihar Kogi, a ranar Lahadi.