Labarin Zomo da Bushiya da Zaki | Aminiya

Labarin Zomo da Bushiya da Zaki

A wani lokaci can da ya gabata Zomo da Bushiya sun taba kulla abota tare da yarjejeniyar taimakon junansu wajen kare kawunansu daga manyan namun daji.

Wata rana sun fita farauta ba su yi nisa a cikin daji ba sai suka yi kicibis da Zaki. Nan suka fadi suka yi gaisuwa ga Sarkin Dawa. Sai Zomo  ya yi sauri ya sha gaban Sarki Zaki ya yi masa alkawarin ba shi wani kaso daga cikin abin da za su samo a wajen farautarsu ta yau, inda shi kuma Zaki ya yi alkawarin ba zai cutar da su ba.

Da farko Bushiya ta ki gaskata alkawarin  Zaki, amma Zomo ya ja ra’ayinta har ta amince. Daga nan sai Zomo ya ja Bushiya zuwa cikin wani rami mai duhu tare da rada mata yadda za ta yi ta fada ciki, sannan shi kuma daga bisani sai ya bi bayan ta. Bayan Bushiya ta fada ne da Zaki ya fahimci cewa wayo suke son yi masa sai nan da nan ya kai wa Zomo wawura inda a take ya lakume shi.

Jin ihun Zomo ya tabbatar wa Bushiya cewa ya shiga komar Zaki, don haka ita kuma ta yi zamanta a cikin ramin nan ta ki fitowa, duk da cewa a tsorace take, amma ta san cewa da wuya Zaki ya kai gare ta. Tun Zaki yana lekawa cikin ramin yana yi mata gurnani har dai ya hakura ya yi tafiyarsa ganin cewa bushiya ba ta da niyyar fitowa, ga shi kuma yana matukar jin yunwa, domin Zomo bai wuce abin kalaci a wurinsa ba.

Duk da bushiya ta ji lokacin da Zaki ya bar wurin, amma hakan bai sa ta yi gaggawar fitowa daga ramin da take boye ba, sanin cewa Zakin zai iya labewa a wani wuri, idan ta fito ya kai mata hari. Sai da dare ya yi, lokacin da Bushiya ta tabbatar Zaki ba ya gani sai ta tashi ta lallaba ta fito a hankali ta kama hanyar gidanta tana tafe tana tunanin yadda Zomo ya yi saurin amincewa Zaki har ya kai shi ya baro.

Darasin labarain:- Ba a saurin amincewa da makiyi.

Da fatan Manyan gobe suna cikin hutu kuma ana taba karatu don kada a manta da abin da aka koya a makaranta.