✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladi Bala ta zama sabuwar shugabar NAWOJ

Bayan gudanar da zabe a kungiyar mata 'yan jarida a jihar Neja, Ladi Bala ta zama sabuwar shugabar kungiyar.

Misis Ladi Bala ta zama sabuwar shugabar Kungiyar Mata ’Yan Jarida (NAWOJ), a taron kungiyar karo na 10 a garin Minna, Jihar Neja.

Ladi Bala wadda ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA Yola ce ta samu kuri’a 439 yayin da ta kayar da Aisha Ibrahim wacce ta samu kuri’a 251 yayin da sauran abokan takarar nasu suka samu kuri’u 100 kowaccensu.

Helen Udofa ce ta zama sabuwar Sakatariyar kungiyar ta kasa, Fatimah Rasheed daga Jihar Kwara kuma ta zama Ma’aji.

Da take jawabi kadan bayan an rantsar da su, Ladi Bala ta yi alkawarin ciyar da kungiyar gaba, musamman ta fannin abin da ya shafi mata ’yan jarida.

Ta kara da cewa zababbun shugabannin za su kasance masu bijiro da sabbin abubuwan cigaba ga ’ya’yan kungiyar.

Har wa yau sabuwar shugabar ta NAWOJ ta ce za su shigar da kungiyar cikin tafiyar masu ruwa da tsaki a aikin jarida a Najeriya.

Ta bayyana cewa za a bi batutuwan da suka shafi iya aiki yadda ya kamata tare da inganta kwarewar aiki tsakanin mata ’yan jarida a Najeria.

Ladi ta kuma bukaci wadanda suka shiga zaben da su hada kai da sabbin shugabannin don ciyar da kungiyar zuwa wani mataki.