✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah

Abubuwan da aka kwadaita Musulumi su aikata a ranar Karamar Sallah

Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci.

Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida —  namiji ko mace.

A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna:

  • Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi.
  • Fitar da zakkar fid da kai, wato Zakkar Kono.
  • Cin dabino ko abinci kafin zuwa Sallar Idi.
  • Yin wankan idi kafin zuwa halartar sallar idi.
  • Sanya sabbi ko mafiya kyawtun tufafi da mutum ya mallaka.
  • Sanya turare da yanke farce
  • Ana son sanya turare ga maza.
  • Yawaitawa da kuma bayyana kabarbari ga maza da mata.
  • Daina yin kabbarori daga lokacin da aka tayar da sallar.
    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, LaiLaha illAllah, Allahu Akbar walillahil hamdu.
  • Sauraron huduba bayan kammala Sallar.
  • Zuwa sallar da dawowa ta hanyoyi daban-daban.
  • Rashin zuwa da makami ko wani abu da zai razana mutane sallar idi.
  • Ziyara da taya ’yan uwa da sauran murna.