✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lafiyata kalau, ku daure ku zabe ni – Tinubu ga ’yan Najeriya

Ya ce aikin da yake nema kwakwalwa yake bukata ba kafa ba.

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana da koshin lafiyar da zai shugabanci Najeriya a zaben shekara ta 2023 mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a Oshogbo, babban birnin Jihar Osun, lokacin da ya ziyarci Fadar Ataoja na Oshogbo ranar Juma’a.

Tinubu, wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas ne, ya ce muddin ’yan Najeriya suka ba shi damar zama Shugaban Kasa a zabe mai zuwa ba za su yi da-na-sani ba.

Ya ce, “Ba aikin birkilanci nake nema ba. Aikin da nake nema kwakwalwa yake bukata. Lafiyata kalau. Kawai aiki aka yi min a kokon gwiwa, kuma na warke.

“Ba tseren doki zan yi ba ballantana a ce kafata ba za ta iya ba. Ina da gudunmawar da zan bayar don ciyar da Najeriya gaba,” inji Tinubu.

Tun da farko dai sai da Tinubu, wanda ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya ziyarci fadar Ooni na Ife da ke Ile-Ife da kuma fadar Owa Obokun Adimula na Ijesa da ke garin Ilesa a Jihar.

Tinubu ya kara da cewa, “Na zo nan ne neman tabarraki da addu’o’inku. Kun riga kun san aniyata, kun san me nake nema. Yanzu abin da nake nema a wajenku kawai shi ne hadin kai da addu’a.

“Na jima ina mara wa mutane baya a nan da can, mun zagaya dukkan lungu da sakon kasar nan wajen tallata ’yan takara, musamman a 2015 da muka tallata Muhammadu Buhari, sannan muka sake yi masa haka a 2019,” inji shi.

A ’yan watannin nan dai an yi ta cece-kuce kan lafiyar Tinubun, inda wasu ke ganin ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai ja ragamar kasar, kari a kan tarin shekaru da tsufan da yake fama da su.

Ko a bara dai sai da ya shafe tsawon watanni yana jinya a Birtaniya, bayan an yi masa aiki a kokon gwiwarsa.

Amma Tinubu ya sha nanatawa a wurare da dama cewa ya warke sarai kuma zai iya jagorantar kasar, kuma tuni ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a babban zaben 2023 mai zuwa.