✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin bacewar shinkafar Kebbi/Legas a kasuwanni

Dambarwar bacewar shinkafar Lake Rice ta hadin gwiwar Jihohin Kebbi da Legas a Kasuwanni

’Yan kasuwa da dillalan shinkafa da dama a Legas da wasu wurare na mamakin yadda shinkafar Lake Rike da ta saba karade kasuwanni a lokacin bukukuwa ta bace bat.

A shekarar 2016, tsohon Gwamnan Legas, Akinwumi Ambode ya yi hadin gwiwa Gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu, don samar da Lake Rice wadda aka yi wa suna ta hanyar hada bakake biyu farkon sunan Jihar Legas (La), da biyun farkon Kebbi (Ke).

Sai dai saukar Ambode daga mulki ke da wuya, sai samuwar shinkafar ta fara wuya, ta yadda alamu ke nuna kamar jihohin biyu sun yi watsi da yarjejeniyar.

An kulla yarjejeniyar ce domin johihin biyu su amfana, kasancewar Jihar Kebbi babbar cibiyar noman shinkafa ce, Legas kuma babbar cibiyar kasuwanci.

Makusanta a yarjejeniyar sun ce an tsara ta ne ta yadda za a shigar da manoman Jihar Kebbi a harkar kasuwancin shinkafar da za su rika samarwa ga masu kasuwancinta a Legas yadda ya kamata.

Yayin da wasu jami’an gwamnati ke cewa tsaikon da aka samu na wucin gadi ce saboda wasu matsololi, wasu na alakanta hakan da siyasa.

Wasu na zargin sabanin Bagudu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC da kuma Jagoran Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu ne ya kawo wa shirin karar kwana.

A ganin wasu kuma, yanayin kasuwa ne ya kawo wa yarjejeniyar cikas.

Shinkafar wadda a lokacin ake sayar da babban buhunta N12,000, karami kuma N6,000, ta samu karbuwa ta yadda ake turuwar sayen ta, musamman a Jihar Legas da makwabtanta a Kudu maso Yamma.

Mun samu arziki da Lake Rice

Amma faduwar Ambode a zaben 2019 ke da wuya, sai ta fara karanci a kasuwanni.

Wasu ’yan kasuwa su bayyana mamakinsu kan yadda shinkafar ta bace a kasuwa bayan faduwar Ambode a zaben 2019.

Wata ’yar kasuwa, Risikat Adam, ta ce:  “Nakan sayi babban buhu N12,000 a wurin gwamanin jiha in sayar N13,000 zuwa N14,000. Karamin buhu mai cin kilogram 10 kuma ana sayarwa N25,500. Mun yaba da shirin domin ya taimaka wajen samar da shinkafa da talaka zai iya saya.”

Wani mai sayar da shinkafar wanda kuma ma’aikacin gwamnati ne, ya ce sukan same ta cikin sauki, har wasunsu na sayar wa kananan dillalai domin su ma su riba.

“Lokacin da Lake Rice ke kasuwa, yawancin mutane na iya sayen ta amma yanzu shinkafa ta yi tsada sosai,” inji shi.

Wani babban dillalin shinkafa, Sulaiman, ya ce watakila yawaitar kamfanonin shinkafa na cikin gida da aka bubbude bayan gwamnati ta rufe iyakokin Najeriya a 2019 ne ya sa batun Lake Rice susucewa.

“Na ji cewa hakan ce ta sa bukatar shinkafa ta karu, Legas ba ta samun adadin da ta saba samu a baya,” inji shi.

“Sannan, a matsayina na mai yin harkar shinkafa iri-iri, akwai shinkafar cikin gida iri-iri da ma suka fi Lake Rice. Da yawa daga cikinsu za su yi gogayya da ita har su cike gibin da aka samu na rashinta a kasuwa, duk da cewa sun dan fi ta tsada.

“Duk da haka, ba za a raba lamarin da siyasa ba, saboda Gwamna Sanwo-Olu na hawa mulki maganar ta shiririce. Da alama ba ya son ci gaba da shirin,” inji dan kasuwar.

Masana

wani kwararre a fannin kasuwannin shinkafa, Tolulope Daramola, ya ce akwai siyasa a cikin sha’anin bacewar LAKE RICE.

Daramola, wanda shi ne ya kafa gidan gonan Menitosh Farm, ya ce duk da cewa gwamantin jihar na kafa kamfanin shinkafarta a Imota, bai kamata a kashe Lake RICE ba.

A cewarsa, maimakon haka, kamata ya yi kamfanin shinkafar na Imota ya zama wani bangare ne na fadada Lake Rice.

“Na san akwai siyasa a ciki, bai kamata tsarin kasuwanci ya rika tangal-tangal ba, amma abin da ake yi a kasar nan ke nan, da zarar an fara wani abu, wata gwamnati na zuwa sai ta dage sai an yi sabo. Gaskiya abin da aka yi a Imota bai kai wancan ba, kamata ya yi Imota ya zama reshen Lake Rice, amma ba wai ya kashe shi ba.”

Manoman shinkafa

Wani manomin shinkafa a Kamba, Jihar Kebbi, Sani Aliyu, ya bayyana takaicin yadda aka bari shirin ya mutu.

“Ban ji dadin yadda shirin ya mutu ba domin a lokacin da aka fara shi, mutane kan zo nan suna neman shinkafa. Wasunmu sun karbi rancen bankuna domin fadada nomamnu, amma bayan ’yan shekaru sai shirin da aka yi na’am da shi ya mutu saboda siysasa,” kamar yadda ya ce.

Aminiya ta yi kokarin tattaunawa da Kwaminshinan Noma na Jihar Legas, Bisola Olusanya, amma ba ta amsa tambayar da muka tura mata ba, haka ma Sakataren Yada Labaranta, Gboyega Akoshile.

Kamfanin shinkafa ta Imota

A watan Disamba 2020 ne aka tsara cewa kamfanin da aka kafa a Imota, mai iya cashe Metric Tonne 32 na shinkafa a awa daya zai fara aiki, amma aka dage lokacin zuwa rubu’in farko na 2021.

A baya, tsohon Kwamishinan Gona na Jihar Legas, Gbolahan Lawal, ya ce idan masana’antar ta fara aiki, za ta rika samar da manyan buhu miliyan 2.4 na shinkafa a shekara, da kuma ayyuka 250,000.

Aminiya ta kasa samun tsohon Gwamna Ambode domin jin ta bakinsa. Kakakinsa, Habib Haruna ma bai amsa bukatarmu ta yin tsokaci game da aikin ba.

Yarjejeniyar ta nan

Wani Shugaban Karmar Hukuma makusancin Ambode, da ya bukaci a saka sunansa ya ce “har yanzu shirin na nan.”

Sai dai ya ce masana’antar shinkafa da ke Imota da gwamnatin jihar ke yi za ta rika samar da kusan ninkin abin da Lake Rice ke samar.

Duk da haka ya ce ba za a rasa siyasa ba wurin janye maganar Lake Rice din.

Ba a amsa sakonninmu ba

Mun nemi jin ina aka kwana game da yarjejeniyar daga Kwamishinan Noma na Jihar Kebbi, Attahiru Maccido, amma ya mu tuntubi wani mai suna Usman Balkore.

Ya ba mu lambar wayar Balkore amma ba ta shiga, kuma Balkoren bai amsa rubutaccen sakon da muka aika masa ba.

Mun tura wa Gwamna Bagudu rubutaccen sako, kan lamarin a ranar Lahadi, amma ba mu samu amsa ba.

Mu kuma tura wa kakakinsa, Yahaya Sarki makamancin sakon, muka kuma kira shi a waya amma bai amsa ba.

A watan Oktoban 2020, Bagudu ya shaida wa wata jarida cewa babu “Babu abin da ya samu yarjejeniyar. Mu ne ba mu noma shinkafar da za ta wadata a kasuwar ba.

“A lokacin da muka kulla yarjejeniyar ba mu da niyyar sayar da shinkafar ba; mun yi ne domin mu tabbatar wa duniya cewa Najeriya za ta iya samar da shinkafa mai inganci.

“Manufar ita ce samar da kafar inganta ta matuka ta yadda ’yan Najeriya za su fahimci irin damar da muke da ita su samun kwarin gwiwa cewa Najeriya za ta iya.

“Yanzu daukacin Najeriya ta gamsu da ingancin shinkafa ’yar gida da ake nomawa a Abakaliki, Ogoni, Kebbi, Jigawa, Taraba, da ko’ina a Najeriya. Manufar yarjejeniyar ta farko ke nan,” inji Bagudu.

Lamarin siyasa

Rahottanni na nuna cewa Bagudu bai ji dadin yadda Tinubu ya kawar da Ambode ba a siyasance a zaben 2019.

Gwamnonin APC sun mara wa Ambode baya a yunkurinsa na neman wa’adin mulki na biyu a Jihar Legas amma shugabanin jam’iyyar a Jihar suka juya masa baya, bisa bukatar Tinubu.

Wata majiya ta ce da Ambode ya samu wa’adin mulki na biyu, da an ci gaba da yin Lake Rice.

Yanzu aka fara shirye-shirye gabanin zaben 2023, an fara hasashen cewa Tinubu zai nemi takarar Shugaba, amma gwamnonin APC da dama na kokarin dakile shi.

Majiyarmu daga cikin magoya bayansa ta shaida mana cewa babu wata manakisa da za ta kawo wa farin jinin Tinubu tangarda.

Wani dan Kungiyar A-Mutun Tinubu a 2023, (TNN), Hon. Kunle Okunola, ya ce tuni ’yan Najeriya suke goyon bayan gwanin nashi.

Aminiya ta tuntunbi kakakin Tinubu, Tunde Rahman, ya kuma tabbatar mata cewa Tinubu ba shi da wata matsala tsakaninsa da Bagudu.