✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lalacewar matatun mai: Majalisa ta gayyaci Shugaban NNPCL

Shugaban NNPCL zai amsa tambayoyi kan lalacewar matatu da satar danyen mai da kuma karancin kudaden shiga daga bangaren

Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kolo Kyari, ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan matsalar satar danyen mai da kuma lalacewar matatun man gwamnatin Najeriya.

Shugaban Kwamitin Man Fetur na Majalisar, Sanata Mohammad Sabo Nakudu, ya ce wajii ne Mele Kyari ya bayyana a gabansu ranar Talata, ya gaya musu me kamfaninsa ke yi don magance satar danyen mai da raguwar kudaden shida daga bangaren da kuma lalacewar matatun mai.

Sanata Nakudu ya gayyaci Mele Kyari ne a lokacin zaman tattaunawar da kwamitin ya yi a Abuja ranar Laraba, kan matsalar satar danyen mai da kuma lalacewar matatun man Najeriya da batun tallafin mai da gwamnati ke yi, da dai sauransu.

Gabanin zaman tattaunawar kwamitin, Daraktan Hulda da Jama’a na kamfanin, Garbadeen Muhammad, ya ce babu wanda NNPCL ya gayyata ko ya rubuta wa takarda a Majalisar.

A cewarsa, Dokar Man Fetur “ta sanya a cikin jerin masu halartar zaman kwamitin Majalisar Dokoki ta Tarayya.

“Mu a NNPCL a shirye muke mu amsa gayyatar duk wani kwamitin Majalisa kan abubuwan da suka danganci ayyukanmu.