✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lallai Buhari ya sa hannu a kan dokar zabe in yana son. . .

Ya zama wajibi Buhari ya gaggauta sa hannu in har yana son kawo gyara a dimokuradiyya.

A kwanakin baya ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da gyaran dokar zabe, a matsayin shirin babban zaben kasa na shekarar 2023, in Allah Ya kai mu.

Kundin Dokar Zaben da akan yi wa kwaskwarima daga lokaci zuwa lokaci, shi ya tanadar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), yadda za ta gudanar da zabe da irin hukunce-hukunce da za a yi wa jam’iyya ko danta ko Baturen zabe da mutanen gari da aka samu da laifin karya ka’idojin zabe da sauran tanade-tanade.

A wannan karo wasu daga cikin sababbin sassan da aka kirkiro a yayin yi wa dokar kwaskwarima da suka fi daukar hankalin su kansu ’yan majalisar da ’yan siyasa da manazarta harkokin siyasar kasar nan da akasarin ’yan kasa, a iya cewa batutuwa biyu ne.

Na farko shi ne, irin yadda majalisar ta amince da yin amfani da tsarin zaben ’yar tinke, ko mu ce kato-bayan-kato, ko macebayan mace, ga duk jam’iyyar da ke son fitar da dan takarar da zai tsaya mata takarar neman kowane irin mukami, daga na Shugaban Kasa, ko Gwamnan Jiha, ko dan Majalisar Dattawa ko dan Majalisar Wakilai zuwa dan Majalisar Dokokin Jiha.

A bisa ga wannan sabon tanadin doka, duk dan jam’iyya da ya mallakii katin jam’iyyarsa, yana da dama da ikon ya hau layi don ya darje ya zabi dan takarar da jam’iyyarsa za ta tsayar daga cikin tarin masu neman takara a inuwarta a daya daga cikin mukaman da na ambata a baya.

Wani sabon sashin dokar zaben shi ne iko da sahalewar da Hukumar INEC ta samu na gudanar da zabe da bayyana sakamakonsa ta hanyar amfani da fasahar zamani, kamar yadda muke gani ko ji ana yi a kasashen da suka ci gaba.

Ko a wadannan sababbin sassa, sashen da ya tanadi fitar da dan takarar jam’iyya ta hanyar ’yar tinki shi ya fi tayar da kura, kasancewar tunda aka fara wannan jamhuriyar, wadansu ’yan kalilan a cikin jam’iyya da ake kira wakilai su suke da wuka da nama wajen zabar wa sauran ’ya’yan jam’iyya dan takara, inda shi kansa mai neman tsayawa takarar yake shiga ya fita wajen ganin dukkan wadannan wakilai da za su zabe shi, ya san su ya kuma tanadi yadda zai mallake su.

A takaicen takaitawa wakilai sayensu ake a duk lokacin da ranar amfaninsu ta zo, kuma wanda tayinsa ya fi yawa da shi ciniki kan fada, ba tsoron Allah bare jin kunyar abin da ka biyo baya.

Sanin amfanin wakilai ya sa a duk lokacin tarurrukan jam’iyyu na zaben shugabanni da wakilai, tun daga kan mazabu zuwa na kananan hukumomi zuwa jihohi, gwamnonin jihohi sukan kankane zabubbukan, ta yadda sai wanda suke so, za a zaba kamar yadda ta bayyana a zabubbukan da Jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar a mazabu da kananan hukumomi da jihohi, wadanda yanzu suka bar baya da kura.

Ko shakka babu wadannan zabubbuka ba su yi wa wadansu tsofaffin gwamnonin jihohi da tsofaffin ministoci da masu ci da wadansu ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa dadi ba ko kadan, kasancewar akasarin gwamnonin ba su ba irin wadannan jigajigan jam’iyyarsu (wadansu ma iyayen gidansu ne na siyasa), ko da wakili daya ba, alhali akasarin wadannan jiga-jigan suna da burin ci gaba da zama shugabanni a jihohinsu ko suna son su ci gaba da tsayawa takara ko dai a kan mukamin da suke kai ko na gaba da shi.

Wannan ya sa a tarurruka da zabubbukan Jam’iyyar APC da suka gabata, irin wadannan jiga-jigai suka gudanar da nasu tarurrukan da zaben nasu shugabannin jam’iyyar a jihohi akalla goma. Jihohin da suka hada da Kano da Legas da Akwa Ibom da Ogun da Osun da Neja da Kwara.

Bisa ga wannan hali da ake ciki bai zama wani abin mamaki ba da Majalisar Dokokin ta zartar da wannan sashi da ya halatta yin ’yar tinki, maimakon yin amfani da wakilai da aka saba a baya.

Yanzu kallo ya koma sama, kasancewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ake jira ya sa wa gyare-gyaren hannu don tabbatar da fara aiki da wannan doka.

Sai dai kuma bisa ga yadda ake kallo, wannan tanadi ba zai yi wa gwamnonin jihohi dadi ba, lura da yadda aka raba su da dimbin ikon da suka dade suna cin gajiyarsa a jihohinsu, na sai wanda suke so za a zaba ya tsaya kowace takara, koda kuwa ta Shugaban Kasa ce.

Wannan fargaba ya sa ake tsammanin gwamnonin za su tunkari Shugaba Buhari, da kada ya sa hannu a gyaran dokar, har sai majalisun sun canja wannan sashe da ya tanadi yin ’yar tinki.

A ra’ayin wannan fili, ya zama wajibi Shugaban Kasa ya gaggauta sa wa wannan gyaran doka hannu in har yana son kawo gyara a tafiyar da wannan mulki na dimokuradiyya, wanda zuwa yanzu yake cike da kama-karya da nuna ni-na-isa da yin amfani da kudi da kullum suke kara yawaita a duk lokacin da jam’iyyun kasar nan suka zo fitar da ’yan takarar da za su tsayar a zabubbuka, ta yadda kai ka ce mulkin dimokuradiyya ba mulkin da kowa ke da ruwa-da-tsaki ba ne, na kowa na da iko da damar ya sa hannunsa.

Idan har Shugaban Kasa ya sa hannu, ya kuma zama wajibi ga Hukumar INEC ta zage dantse wajen sa idanu a dukkan zabubbukan fitar da gwani (ta ’yar tinki) da jam’iyyu za su gudanar.

Da wannan doka nake ganin Hukumar INEC ta daina nade hannunta wajen zaman jiran sai dan takarar da jam’iyya ta mika mata zai tsaya zabe kamar yadda yake yanzu.

Su ma gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyu da shugabanni da magoya baya da mabiya, ya kamata su kama ta yadda za a gyara wannan mulki na dimokradiyya ta wannan doka, don kuwa ba haka za mu yi ta zama ba.