Daily Trust Aminiya - Lalong ya kaddamar da kwamitin binciken zaluncin SARS
Subscribe

Lalong ya kaddamar da kwamitin binciken zaluncin SARS

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya kaddamar da kwamitin sauraron koke-koken mutanen jihar da jami’an rundunar SARS da aka rushe suka zalunta.

Gwamnan ya kaddamar da ’yan kwamitin ne a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos, a ranar litinin din nan.

’Yan kwamitin sun hada da Mai Shari’a Philomena Lot mai ritaya, a matsayin shugaban, sai kuma CP Garba Patrick mai ritaya, Ezekiel Dauda Daschen, Misis Rauta Dakok, Misis Kiyenpiya Mafuyai, Dokta John Jinung,m da Fatimah Suleiman.

Da yake jawabi, Lalong ya ce kafa kwamitin ya zama wajibi musamman duba da koke-koken al’umm kan irin miyagun ayyukan da wasu bata-garin jami’an SARS suka aikata.

Ya ce hakan ce ta sanya Gwamnatin Tarayya rushe SARS kamar yadda masu zanga-zangar a sassan Nejeriya suka bukata.

“Masu zanga-zangar sun kawo wa gwamnati bukatar a soke rundunar, a hukumta jami’an da suka zalunci jama’a tare biyan diyya ga wadanda aka zalunta.

“Don haka muka kafa wannan kwamiti domin sauraron koke-koken dukkannin mutanen da jami’an na SARS suka zalunta a jihar nan’’, inji Lalong.

Ya bayyana cewa ayyukan kwamitin sun hada da binciko koke-koken wadanda aka zalunta a jihar, kawo shaidun wadanda aka zalunta, da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a biya diyya ga wadanda aka zalunta.

Ya yi kira ga masu zanga-zanga su kaurace wa tituna, su mayar da hankalin zuwa ga kwamiti domin gabatar da korafe-korafensu.

An debar wa kwamitin wa’adin wata shida don kammala aiki da aka ba shi.

More Stories