✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lambar NIN: Za a dakatar da rajista saboda COVID-19 —Minista

Ana iya dakatarwa a sake tsari don kauce wa yaduwar COVID-19

Minista a Ma’akatar Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce Gwamnatin Tarayya na iya dakatar da aikin rajistar lambar shaidar dan kasa (NIN) da ke gudana.

Ministan ya ce Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) na bukatar ta sake tsara yadda aikin zai gudana domin tabbatar da kariyar masu zuwa yin rajista ba tare da an yada cutar COVID-19 ba.

Da yake magana kan hotunan dandazon jama’a a cibiyoyin rajistar NIN na NIMC, Ministan ya ce, “Ban ji dadin ganin yadda mutane suka taru ba da yawa tamkar wani babban taron yada cutar, wanda ba a fatar hakan.”

“Na tabbatar cewa ma’aikatar da ta dace, wadda ita ce ta Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani tana duba lamarin.

“Ina ganin za a iya dakatar da shirin don sake tsara shi ta yadda za a gudanar da taron mutanen saboda ba da niyyar a samu cincirindon jama’a aka tsara shi ba,” inji Mamora.

Da yake magana a shirin tashar Talabijin na Channels, a ranar Litinin, ministan ya ce yin hakan shi ne zai ba da damar kauce wa yaduwar COVID-19 a wuraren yin rajistar.

“A matsayinmu na Gwamnati, muna da aiki don tabbatar da cewa mutane ba su kamu ba.

“Har ila yau, aikinmu ne mu mu tabbatar mutane sun bi ka’idar abin da zai amfani al’umma gaba daya,” inji shi.

Jama’a sun yi ta dafifi zuwa cibiyoyin rajistar NIN bayan da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanya wa kamfanonin sadarwa wa’adin rufe du layukan waya marasa rajista lambar NIN.

Idan ba a manta ba ma’aikatan NIMC sun yi yajin aikin gargadi na kwana biyu saboda “neman a biya bukatunsu na kudaden da suke gbin gwamnati, yashin ingancin yanayin aikinsu da kuma kariyarsu daga barazanar kamuwa da cutar COVID-19”.

Bayan dakatar da yajin aikin a ranar Juma’a, ma’aikatan sun bayar da wa’adin mako biyu ga gwamnati ta biya bukatunsu domin guje wa sabon yajin aiki.