✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lasisin tuka A Daidata Sahu ya koma N100,000 —KAROTA

Duk wadanda ba su yi rajistar tun a baya, to kuwa a yanzu duk mai so ya koma Naira dubu dari.

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta ce daga yanzu duk masu bukatar lasisin tuka babur din ‘A Daidaita Sahu’ a Jihar dole ne su biya Naira dubu dari madadin Naira dubu takwas da ake biya a baya.

Shugaban Hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ne ya sanar da hakan a  yayin ganawarsa da manema labarai ranar Laraba a birnin Dabo.

Ya ce, “Duk wadanda ba su yi rajistar neman izinin tuka babur mai kafa uku tun a baya ba, to kuwa a yanzu duk mai so ya koma Naira dubu dari,” a cewarsa.

Ya ce sun baza jami’ansu domin lura da kuma cafke wadanda ba su da lasisin da zummar daukar mataki a kansu.

A cewarsa, Gwamnatin Jihar ta bayar da isasshen lokaci amma wasu masu kunnen kashi suka suka ki yi a kan lokacin da aka bayar.

Dan Agundi ya ce a yanzu akwai baburan ‘A Daidaita Sahu’ dubu sittin masu lasisi da ake harkokin sufuri da su a Jihar Kano.

Dangane da batun karbar haraji, Dan Agundi ya ce Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano ce ke da alhakin karba a yayin da nauyin da rataya a kan tasu hukumar ya takaita kadai a kan aiwatarwa.