✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lauya ya kai karar iyayensa kan rashin tallafa masa da kudi

Wani babban lauya mai shekara 41 ya kai iyayensa kara kotu, yana neman a tilasta musu su ci gaba da daukar dawainiyarsa da dukiyar da…

Wani babban lauya mai shekara 41 ya kai iyayensa kara kotu, yana neman a tilasta musu su ci gaba da daukar dawainiyarsa da dukiyar da suke da ita har karshen rayuwarsa.

Lauyan wanda aka sakaya sunansa, ya shigar da karar iyayensa ne saboda ya dade yana dogara da su sama da shekara 20 da suka wuce, sai a cikin kwanakin nan ne suka rage tallafin kudin da suke ba shi bayan alakarsu ta yi tsami.

Ya bukaci alkalin kotun da ya umarci iyayensa su ci gaba da tallafa masa da dukiyarsu, inda lauyoyin da suke kare shi, suka karanta dokokin da suke da alaka da aure da dangantakar ’ya’ya da iyaye lokacin da ake sauraren karar.

Abin mamakin ma shi ne lauyan yana aiki a matsayin mai zaman kansa, kuma ya kama ofishin da yake biyan haya a cikin birnin Landan wanda ginin mallakin iyayensa ne, kuma iyayen sun dade suna biya masa kudaden hayar ofishin, amma duk da haka ba su  gamsar da dan nasu ba.

A cewar Mai shari’a James Munby, “Iyayen da aka kai karar sun dade tsawon shekaru suna taimakon dansu da ya kai su karar.

“Tun da farko iyayen sun kyale dan nasu ya ci gaba da zama a gidansu da ke tsakiyar birnin Landan wanda aka yi wa rajista a matsayin ginin da doka ta bai wa damar mallaka, kuma sun dade suna daukar nauyin biyan kudaden harajin gidan”.

Karar da ya shigar na da nasaba ce da rage taimakon kudin da iyayen suka saba yi masa, sai dai akwai yiwuwar cewa samunsa ya ragu ne don haka taimakon da suke ba shi shi ma ya ragu, bayan sabon da suka yi masa na sama da shekara 20 suna yi masa hidima wanda hakan  ya sa ya dogara kacokan a kansu.

Su dai iyayen lauyan yanzu haka suna zaune ne a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma sun bukaci kotun ta yi watsi da karar, kamar yadda Mai Shari’a James Munby ya ce a takaita shari’ar sannan a yi watsi da ita.

Wannan ba shi ba ne karo na farko da aka taba samun wani ya kai iyayensa a kotu don tilasta su ci gaba da tallafa masa da kudi  inda ko a watan Agusta a kasar Italiya, wata babbar kotu ta yanke hukunci kan wani matashi mai shekara 35 cewa bai zama dole iyayensa su ci gaba da tallafa masa da kudi ba.

Ana samun rahotannin matasa masu son iyaye su ci gaba da taimakonsu da kudi bayan sun girma.

A shekarun baya an samu iyayen da suka shigar da karar dansu saboda kin barin gidansu.

Sai a watan jiya aka samu wani saurayi da ya kai karar mahaifiyarsa kotu saboda ta kore shi daga gidanta kamar yadda Aminiya ta wallafa makonni uku da suka gabata.