✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lawurjen lankwasar laujen laftun lamuni

Lamirin larurar lamarin lamuni Langabun lankwasar lagwani Lankwayar laushin lawashin launi Luguiguita lawurjen laftun bini-bini Lalitar lafkewar iyaye da kakanni   Rakiyar raka-rakar rankon rance…

Lamirin larurar lamarin lamuni

Langabun lankwasar lagwani

Lankwayar laushin lawashin launi

Luguiguita lawurjen laftun bini-bini

Lalitar lafkewar iyaye da kakanni

 

Rakiyar raka-rakar rankon rance

Rugu-rugun ribace-ribace

Romon ragowar rummace

Rangajin rarumar rakice-rakice

Rugugin rudanin rikice-rikice

 

Ana ta kai-kawo

Laluben bashin je-ka-ka-dawo

Asusun kawo-kawo

A zubo kindirimon damun dawo

Sai a huta da yawo

 

Ana ta yayin tufa mai maho

Ba ruwan kowa ko oho

Masu fuka-fukin tashi da tsoho

Da bala’i ya tunkaro ai goho

Alhali magabta sun yashe dami a sanho

 

Ana ta gyare-gyare

Amma irin na kurege da gyare

Marasa kishi na son a dare

Yadda suka ga rana haka suka ga dare

Kwasar kudi sai sun karkare

 

Tituna da kwazazzabai

An kwashe damin matsabbai

Jami’an tsoro na kwasar ’yan kwabbai

Hadurra na haifar da tabbai

Al’ummar kasa an nunke mu a baibai

 

’Yan matan jaba da beran dunka

An sha duka

Talaka ya fi su shan tafka

Rani damina da kaka

Ana ta haka-haka

 

An tara dimbin haraji

Ga bashi ya zame mana hanji

Karfin kasa yai kasaitar tada kwanji

Amma ana fama da kululun kurji

Karin kiyayyar karyar karaji

 

An garkame gambun iyaka

Makwafta na tufka tufka

Makarkashiyar muku-mukun marka-marka

Kowa bai shakka

An fantsama gayaunar garka

 

 

Dokta Uban-diya

Ya bankado tsirin tsiya

Basussukan bibiyar baya

Da karin masu zirya

Mai liyafar uwar jiki yai tambaya

 

Baban-burin-huriyya

Anai maka tariya

Masana tattalin tulin dukiya

Kai kasake da na-zomon zamiya

Ka bi kadin dubi da na-nujiya

 

Farin farawa

Mun jefi mugun

An kama mana kugun

Yanzu muna bundun-bundun

Haba Haurobiyawan

 

Cikin shekaru kofar hancin zagaye

An darkake Dalar daloli

Taraliyar tattali

Tuttule tulu tuli-tuli

An zo ana ta kewaye-kewaye

 

Balulluba

Ko kassaba

Kar a ce an yi kwaba

Masana sun sassaba

Bashin man dangwali yaba

 

Dundumin dumuiniyar duniya

Dagar dogewar danniya

Daure-dauren dorin dirkaniya

Dari-darin daukar dawainiya

Dawurwurin darkake damin dukiya

 

An gaji gashin balama kwanciyar magirbi

An kai tulin kwatanccen magirbi da magirbi

Adadin yawan abin da ake bi

Za a karo kari ai ta bi

Mahukunta saran gatari sai da dubi

 

Majalisa na nazari

Za tai bin kadin dan mazari

Ko za su lalubi guzuri

Dankari makari

Mu nai musu barka da kokari

 

Kar a kara mana sasari

A zo anai mana kirari

Bashi hanji ne

In yawansa ya kankane

Sai kasa ta afka garari

 

An dai yi jimiri

Lallai a sake shiri

Kar ai mana sihiri

Dukiya anai mata cin birbiri

An gaza sake zane kiri-kiri

 

An kwaso zinari

Lu’u-lu’u da jauhari

Tunkuza ta daina zaman fahari

Garkar gayauna ake yunkuri

Dole shugaba ya zam zakakuri

 

Tumbatsar tulin tururuwar lankwasar laftun lamunin Haurobiya a karkashin jan ragamar Baban-burin-huriyya masana sun fasko cewa lamarin ya ta’azzara, musamman ganin yadda aka tunkuda wa Majalisar Dokokin Kasa ta amince a jinko mana LAWURJEN LAFTUN LAMUSHE-LAMUSHEN LAKUME LAMURJEN LAMUNI na Dala kofar hanci da zagaye ba wani zagaye-zagaye. Wannan lamari ya haifar da takaddamar ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan musamman rukunin wadanda ke ninkayar nunin cewa har yau ba ta sake zane ba, ko ba su gani a kasa ba. Har yanzu dai Gwamnatin Baban-burin-huriyya ba ta nusar da al’umma irin dimbin alfanu da ke tattare da LAFTUN LUGUDEN LAMUNI, ballantana a tabbatar babu WALLE-WALLEN WULWULAWAR WALA-WALAR WUCCIKEWAR WA-KA-CI-KA-TASHI.

Wani rukunin gama-garin jama’a na nuna firgicinsu ne kan ka da Baban-burin-huriyya ya kammala wa’addin mulkinsa ya bar kasa tana BUNDUN-BUNDUN din iyon ninkayar  BIDIRIN BIREDEN BULULLUBAR BASUSSUKAN da WUNI-WUNINSU YA ZARTA NA ’YAN UWAN DA BA SU DA WANI.

Su kuwa rukunin masana a fannin tarin tulin tattala dukiya, irin su Dokta Uban-diyya Mailiyafa (ta uwar jiki), wanda ya kasance masanin fannin tsimi da tanadi, kuma tsohon Mataimakin Gwamna gwarangwam na Babban Asusun Alkinta dukiyar Haurobiya, tsokale-tsokalen tsokacin tsagwaron BIDIRIN BIREDEN BUNKASAR BASUSSUKAN BUNDUN-BUNDUN, inda har ya yi korafi kan cewa, “lallai akwai bukatar a bijiro da tambayar tantagaryar taratsin titsiye ga Jam’iyyar tsintsiyar laushi da kwakwa, har ma da uban gayya, wato Baban-burin-huriyya, kan yadda aka yi cikin shekaru tsayuwa bisa kafa guda suka jibga wa kasar nan laftun lamunin basussukan bundun-bundun da doriyar Dala gashin balama kwanciyar magirbi da zagaye kan abin da suka gada na Dala gashin balama kwanciyar magirbi kacal?”

Wani hanzari ba rarewa a arce a guje ba, tuni na jiwo daga Baban-burin-huriyya cewa, “tarin tulin tattalin kudin tunkuzar kasar nan ba za su iya biyan dimbin bukatun al’ummar kasa wajen samar da kayan  MOTSIN MUKA-MUKIN MURMUSHIN MURMUREWAR MORI-MORIN MOREWAR rayuwa, musamman hanyoyin ababen tattakin balaguro da farfajiyar bokan Turai da hana zaman kashe fatari (a tsakanin masu fuka-fukin tashi)  da samar da cika-cikin ci-makar cikakken tsarin tsaron tsare tsoro da inganta Ingausar ison isar da sakonnin farfajiyar koyon watsattsake da wangale wagagaen litattafai.”

Bisa la’akari da al’amuran da ke wakana game da LAMIRIN LAMARIN LAMUNI LANGABUN LANKWASAR LAGWANI, al’amari ne da ke nuni da liliyawar laushin lawashin launin luguiguita laftun bini-bini a lalitar lakakin  lafkewar iyaye da kakanni, wato tun daga zamanin jan ragamar baraden bindiga da shugabani kofar hanci na jam’iyya mai danboto da sanda jirge (Baba-ojo da ’Yar’bishiya da Jona-tantin mulki) daukacin kwashe-kwashen da suka yi a LANGAR LIGIDIN LALLAGA LAMUNIN LAGAD, ba su jinko wa kasar nan tsirin tsatsubar tsunburburar tsatsunburun ba.

A matsayina na babban Direban alli, ina ganin babu sasarin sarkakiya game da lullumin lumanar lafto lamuni, ko BIDIRIN BIREDEN BULKALAR BALULLUBAR BASUSSUKAN BUNDUN-BUDUN, matukar dai za a sayar da daukacin matsabban dungurungum wajen bunkasa kasa. Sannan tarin harajin da aka tara, matukar aka sarayar da daukacinsa wajen kyautata rayuwar al’umma, sauran da ya rage sai a yi rankon rubdugun bashi, kun ga ai sai mu ce sambarka!

’Yan makarantar Dodorido mahayan shorido, ku sani cewa, ni ba ni da FIRGICIN FARGABAR FAGAMNIYAR FANGIMAR gama-garin al’umma da ta masana tattalin tulin tarin dukiya. Sai dai abin da na fi jiye mana shi ne, ka da Baba ya karkare mulkinsa ya tara dimbin matsabbai, musamman karime-karimen da ya yiwo daga hannun SAMARIN-KUSU DA ’YAN MATAN JABA DA GAFIYA, har ma da BERAN DUNKA, uwa-uba ga tarin haraji da kudin shiga da hukumar dakile fasa-kwauri ta alkinta wa kasa. Domin in har ba a yi sa’a ba, miyagu na iya sake yin ganganko su zo su sake wawushe lalita karkaf, su kwashe komai-da-komai kakaf.

Haurobiyawa, muna sa ran cewa Baban-burin -huriyya zai yi SABATTA-JUYATTA, wato wadannan matsabbai da ya wafto daga wadanda suka tatuke kasar nan, su za a yi raka-rakar rarakar rankon rancen birimar bunkasar basussuka da  su. Idan an kara samun dimbin ragowar matsabbai akwai yiwuwar Baban-burin-huriyya ya tattara kudin ya yi aikin gina biranen kasar nan su koma kamar birnin LANTSANDAN; shi ke nan ko shugaban kasarmu, ko na wata kasa idan akwai mai muradi, sai kawai ya yi LAFKEWAR LAKAKIN LABE-LABEN LOKON LULLUBEWAR LULLUMIN LUMANAR LUNGUNAN LANTSANDAN!