✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lebanon: Sama da mutum 300,000 sun rasa muhallansu a Beirut

Iftila'in ya hallaka sama da mutum 100 wasu 4,000 kuma na kwance a asibiti

Hukumomi a Lebanon sun ce kimanin mutane 300,000 ne fashe-fashen birnin Beirut suka raba da muhallansu tare da janyo asarar dukiyar da ta kai sama da Dala biliyan uku.

Gwamnan birnin na Beirut, Marwan Aboud, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Laraba cewa fashewar ta kuma hallaka sama da mutum 100, yawancinsu a kusa da babbar tashar jiragen ruwa tare da yin illa ga kusan rabin birnin.

“Ina jin mutum 250,000 zuwa 300,000 ne yanzu ba su da muhalli”, inji shi.

Fashewar dai ta kara jefa kasar, wadda da ma take cikin tashin-tashina, cikin wani sabon halin kaka-ni-ka-yi.

Tuni dai rahotanni suka tabbatar da isar jami’an bayar da agajin gaggawa daga kasar Kuwait da sanyin safiyar Laraba.

Kungiyar agaji ta Red Cross a kasar ta ce yanzu haka mutane sama da 4,000 na can suna samun kulawar gaggawa sakamakon munanan raunukan da suka ji.

Firaministan Lebanon Hassan Diab ya yi kira ga kasashe kawayen kasar tasa, wadda take kokarin murmurewa daga koma-bayan tattalin arzikin da ta fada da kuma annobar COVID-19, da su tallafa mata.

Sojojin kasar Lebanon dauke da wani daga cikin mutanen da suka ceto bayan ya makale a karkashin gini sakamakon iftila’in.

Kasashe na ta mika sakonnin jaje

A hannu guda kuma, kasashe na ci gaba da yi wa Lebanon jaje bayan mummunan iftila’in fashe-fashen da ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyi da dama a birnin Beirut.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani da Sarki Abdullah na Biyu na Jordan sun ce za su aike wa Lebanon agaji musamman ta bangaren lafiya.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ma ya aike da ta’aziyyarsa kan mummunar fashewar da ta afka wa birnin na Beirut.

Mista Zarif ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba cewa, “Muna mika ta’aziyyarmu da juyayinmu ga al’ummar Lebanon, komai zai wuce”.

Yadda wuta ta kama gine-gine bayan fashewar sinadaran

Su ma a nasu bangaren, kasashen yankin Gulf sun sanar da bayar da nasu tallafin, inda kasar Qatar za ta tura asibitocin tafi-da-gidanka don tallafa wa kasar.

Kasar Saudiyya kuwa cewa ta yi tana bin diddgin lamarin cikin taka-tsantsan.

Kazalika, a wani mataki na ba saban ba, kasar Isra’ila wacce ba ta ga maciji da Lebanon din ta yi alkawarin kai kayan tallafi.

Ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz da takwaransa na harkokin waje Gabi Ashkenazi sun ce, “A madadin gwamnatin Isra’ila, ta hannun masu shiga tsakani na kasa da kasa, za mu aike da kayan agajin gaggawa da na asibiti ga Lebanon”.

‘A kai kasuwa’

Sai dai kasar ta Lebanon ta ce a kai kasuwa, tana mai cewa ba yadda za a yi ta karbi tallafi daga abokiyar gabarta.

Baraguzen gine-ginen da fashewar ta yi sanadiyya

Shi kuwa babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, mika sakon ta’aziyyarsa ya yi ga kasar kan abin da ya kira mummunan iftila’i wanda ya ce ya ma shafi wasu daga cikin jami’ansu.

Shugaban Amurka Donald Trump kuwa cewa ya yi fashe-fashen sun yi kama da wani mummunan hari, yana mai cewa manyan hafsoshin tsaron kasarsa sun shaida masa cewa fashewar wasu bama-bamai ce ta haddasa lamarin ko da dai ya ce har yanzu ba a tabbatr da hakan ba.

Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani da jagoran Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum fatan murmurewa cikin gaggawa suka yi wa wadanda iftila’in ya shafa tare da mika ta’aziyyarsu ga kasar.

Shugaba Bashar Al-Asad na Syria, da Shugaba Vladimir Putinm na Rasha da Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson duk sun nuna alhininsu ga kasar.

Emmanuel Macron na Farnasa kuwa cewa ya yi kamar kullum, wannan karon ma kasarsa na tare da Lebanon.

Ya kuma ce jiragen yaki guda biyu makare da kayan agajin da nauyinsu ya kai ton 15, tawagar kwararrun liktoci tare da asibitocin tafi-da-gidanka za su bar Faransa zuwa Lebanon din ranar Laraba domin kai tallafi.