✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lebanon ta sanya dokar ta baci a Beirut

Gwamnatin Lebanon ta sanya dokar ta baci na sati biyu a Beirut tare umartar a tsare dukkannin masu hannu a ajiyar sunadarin ammonium nitrate wanda…

Gwamnatin Lebanon ta sanya dokar ta baci na sati biyu a Beirut tare umartar a tsare dukkannin masu hannu a ajiyar sunadarin ammonium nitrate wanda fashewarsa ta kashe mutum 100.

Wasu mutum 4,000 sun jikkata a iftila’in wanda raba wasu 300,000 da muhallansu.

Majalisar kasar ta ce, “Muna kira rundunar soji ta tsare dukkannin masu hannu a ajiyar ammonium nitrate” a tashar jirgin ruwa na Beirut da ya fashe din.

“Kiyasin barnar ta ranar Talata ya yi kai daga Dala biyan uku zuwa biyan”, inji Gwamnan Beirut Marwan Aboud wanda ya ce fashewar ta yi barna a rabin birnin.

Faransa ta ce za ta aika jirage uku na ma’aikatan ceto da kayan asibiti da matsayin gudunmuwa ga Lebabon.

Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da haka bayan ya jajenta wa Shugaban Lebanon, Michel Aoun, ta waya bisa tashin iftila’in.

Fadar Gwamnatin Faransa ta Elysee ta ce Macron zai je Beirut ranar Alhamis, inda zai gana da shugabannin kasar ciki har da firai ministan  Hassan Diab.

A yammacin Talata 4 ga Agusta ne aka samu fashe-fashe guda biyu a tashar jirgin ruwa da ke Beirut, babban birnin kasar Labonon.

Lamarin ya yi barna mai yawan gaske a birnin yayin da wutar ta aka yi ta kokarin kashewa da jiragen sama ta ci gaba da ci har zuwa ranar Laraba.

Kasashen duniya na ci gaba da jajanta wa kasar tare da kokarin ganin yadda za su tallafa.