✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Legas ta lashe gasar damben hukumar NBF

Yan wasan damben zamani da ke wakiltar Jihar Legas sun lashe gasar damben zamani da hukumar dambe ta kasa (NBF) ta shirya na shekarar 2013…

Yan wasan damben zamani da ke wakiltar Jihar Legas sun lashe gasar damben zamani da hukumar dambe ta kasa (NBF) ta shirya na shekarar 2013 wanda aka gudanar a karshen makon da ya gabata a babban filin  wasa na jihar.
Jihar Legas ita ta mamaye komai a wasan inda ta lashe lambar zinare biyar da Azurfa daya da kuma Tagulla daya a yayin gasar.
Jihar ta samu nasarar ce a bangeran maza masu nauyin kilo 60 da masu nauyin kilo 64 da kuma masu nauyin kilo 69. Sannan jihar ta samu nasara a bangaren mata masu nauyin kilo 75.
’Yan wasan Jihar Legas sun nuna bajinta yayin da wanda yake wakiltar jihar a bangaren maza mai suna Oto Joseph ya lallasa abokin karawarsa mai wakiltar rundunar sojan Najeriya mai suna Nkem Sunday.
Shi kuwa Olaide Fijab da ke ajin masu karamin nauyi ya buge abokin karawarsa mai suna Olaiya Awosu na Jihar Kuros Riba inda ya lashe kyautar zinare.
Abua Christian daga Jihar Legas ya samu nasara a kan Adeniyi Korede daga Jihar Kogi a bangaren masu nauyin kilo 69, yayin da Francis Gabreil ya doke Akanji Monsuru na hukumar NSCDC kuma ya lashe kyautar zinare a ajin masu nauyin kilo 91.
A bangaren mata masu nauyin kilo 75 kuwa,  Jihar Legas ta lashe zinare inda Teniola Are ta samu nasara da maki 2-1 a kan abokiyar karawarta mai suna Milicent Agboegbulem daga Jihar Delta.
A yayin gasar Jihar Ondo ta samu kyautar azurfa daya da zinare biyu da tagulla daya. Ita kuwa hukumar NSCDC ta samu kyautar zinare daya da azurfa biyu da tagulla daya wanda hakan ya sa ta zo ta uku a jerin wadanda suka samu kyaututtukan.
’Yan wasan Legas da suka samu nasara sun bayyana farin cikinsu da Allah ya ba su sa’a a gasar.  Su kuwa wadanda ba su yi nasara ba sun nuna bakin cikinsu amma sun yi alwashin samun nasara a gasa ta gaba.