✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Libya na bikin tunawa da kifar da gwamnatin Gaddafi

Shekara 11 da kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Muammar Gaddafi

Al’ummar kasar Libya sun shirya gudanar da bikin cika shekara 11 da juyin-juya-halin da aka yi wa Shugaba Muammar Gaddafi kisan gilla.

A ranar Juma’a aka shirya gudanar da kade-kade, raye-raye da wasan tartsatsin wuta har na tsawon kwana guda, bayan cika shekara 11 da kisan Gaddafi.

An kawata babban birnin kasar, Tripoli da tutocin kasar masu launin ja, baki da kore da aka amince da su bayan faduwar Gaddafi.

A ranar Alhamis al’ummar Libya suka yi bikin tunawa da juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Gaddafi, shekara 11 da suka wuce, sai dai har yanzu dimokuradiyyar da suka fata ba ta samu ba, a yayin da wasu ke fargabar dawowar rikici.

Libya ta cika shekara 11 da faruwar wannan al’amari ne a daidai lokacin da kasar ta shafe shekaru tana fama da rarrabuwar kai a tsakanin al’ummar gabashi da yammacin kasar.

Hakan ya sanya kasar samun Fira Minista biyu masu hamayya da juna a lokaci guda, wadanda ke zaune a babban birnin kasar, Tripoli.

A makonni bayan da majalisar dokokin da ke zaune a yankin Gabashin kasar ta dage zaben ranar 24 ga watan Disamba na amincewa da nadin  tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Fathi Bashgha, don ya  maye gurbin gwamnatin hadin kan kasar na wucin gadi, amma Fira Misnita mai barin gado, Abdulhamid Dbeibah, ya ki aminta da hukuncin.