✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun janye yajin aikinsu

Bayan shafe kusan mako daya tana gudanar da yajin aiki, Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta kawo karshensa ranar Lahadi. Jawabin yana…

Bayan shafe kusan mako daya tana gudanar da yajin aiki, Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta kawo karshensa ranar Lahadi.

Jawabin yana kunshe ne a Takaddar bayan taron Kungiyar da Shugabanta Dr. Aliyu Sokomba ya karanta wa ‘yan jarida a Abuja.

Ya ce likitocin sun janye yajin aikin ne domin ba wa mahukumta damar cika alkawuran da suka yi na shuruddan da suka gindaya.

Suka kuma kara da cewar hakan ya faru ne sakamakon rokon da shugaban Majalissar Tarayya, Femi Gbajabiamila da Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Gwamnonin Najeriya da dai sauransu suka yi musu na su janye yajin aikin.

Sakamakon tattaunawar dai, gwamnonin cikin wata sanarwa sun ce likitocin sun amince su janye yajin aikin.

Gabanin haka, sanarwar Bayan taron gwamnoni da Likitocin ta ce, “Gwamnoni sun cimma matsaya da kungiyar likitocin kuma sun amince su janye yajin aikin daga farkon mako mai kamawa sakamakon tattaunawar da suka yi da gwamnoni ranar Asabar, 20 ga watan Yuni.

“Wannan dai shi ne karo na farko da likitocin suka kawo kokensu gaban gwamnonin.

“Shugaban kungiyar gamnonin kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi alakawarin sake zama da kungiyar a cikin mako mai kamawa don duba koke-kokensu, don magancewa.

‘Likitocin, karkashin jagorancin shugabansu na kasa, Aliyu Sokomba da Magatakardarsu, Dakta Bilkisu sun bar sakatariyar kungiyar gwamnonin da alkawarin za su tuntubi sauran mambobinsu su kuma jira su ga abinda gwamnonin za su yi.

“A kan haka ne jagoran kungiyar likitocin ya kira shugaban gwamnonin da yammacin ranar Asabar ya shaida masa sun amince su janye yajin aikin”, inji sanarwar.