✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun janye yajin aiki

A cewarsa, “Mun dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni hudu masu zuwa.”

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin da ta tsunduma ranar daya ga watan Afrilun 2021.

Shugaban Kungiyar, Dakta Uyilawa Okhuaihesuyi shine ya tabbatarwa da Aminiya hakan da ta wayar salula.

Ya ce sun yanke hukuncin dakatar da yajin aikin ne yayin wani taron Majalisar Zartarwar Kungiyar ta kasa wanda ya gudana da yammacin ranar Asabar a Abuja.

A cewarsa, “Mun dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni hudu masu zuwa.”

Dakta Uyilawa ya ce an kuma yi alkawarin biyan hakkokin dukkan mambobin kungiyar nan da ranar Litinin mai zuwa.

“Dukkan mambobinmu dake kan tsarin biyan albashi na GIFMIS za a mayar da su IPPIS, kuma nan ba da jimawa ba za a biya su dukkan hakkokinsu. Wadanda har yanzu suke bin cikason hakkokinsu tun 2020 za a biya su daga kwarya-kwaryar kasafin kudin 2021. An riga an kammala magana a kan biyan kudaden MRTF, yayin da za a kara kudaden alawus na hadurra kowanne lokaci daga yanzu,” inji shi.

Tun da farko dai sai da kungiyar ta tattauna da Gwamnatin Tarayya na tsawon sa’o’i da dama a ranar Juma’a kafin ta yanke shawarar janye yajin aikin.