✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Likitoci sun sa wa mutum kodar alade a Amurka

Ana fatan hakan zai kawo karshen karancin taimakon koda da ake samu a wannan lokaci.

A karon farko wani kwararre a fannin tiyata a Amurka mai suna Dokta Robert Montgomery ya ce, sun samu nasarar dasa wa wani mutum kodar alade, inda suke fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen karancin taimakon koda da ake samu a wannan lokaci.

Kwakwlwar mutumin da aka sanya kodar tuni ta daina aiki, inda yake ci gaba da rayuwa da taimakon na’ura, lamarin da ya sa mutum ne da kwakwalwarsa ta daina aiki, lamarin da ya sa aka cire tsammani da shi.

Ita dai kodar da aka yi amfani da ita, ta wani alade ne da aka jirkita domin ta dace da halittar jikin dan Adam ta yadda ba za ta zama wani bakon abu ba, balle kwayoyin kariya su yake ta.

An gudanar da tiyatar a Jami’ar New York tsawon awa biyu, inda masu tiyatar suka hada da kodar aladen da ake bayar da jijiyoyin jinin kwakwalwar mutum domin tabbatar da ko za ta yi aiki yadda ake bukata ko kuma akasin hakan.

Har yanzu ba a yi wa aikin kallo na tsanaki ba ko kuma a wallafa shi a mujallu da jaridu, amma akwai shirin yin hakan nan gaba.

Masana harkar lafiya sun ce zuwa yanzu wannan ne aiki mafi girma da aka yi a wannan fanni.

An taba yin gwajin irin wannan a kan birai, amma gwajin ba a taba yi ba a kan mutane.

Ba wani bakon abu ba ne amfani da sassan jikin alade domin dasa wa dan Adam.

Tuntuni an jima ana dasa wa dan Adam bututun da ke kai wa zuciya numfashi.

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai kuma wasu sassan da za su dace da dan Adam musamman a bangaren girma.

Bayan gudanar da tiyatar, likitocin sun yi sama da kwana biyu suna nazarin yadda kodar ke aiki, sannan suna ci gaba da gwaje-gwaje iri-iri.

Kwararren likitan da ya jagoranci aikin Dakta Robert ya shaida wa BBC cewa, “Mun rika bibiyar yadda kodar ke aiki na awanni, kuma tana aiki kamar ta dan Adam, wato duk abin da kodar mutum ke yi ita ma tana yi.

“Tana aiki sosai, kuma babu alamun za ta kawo wata matsala a nan gaba.”

“Zamanin a kashe wani a raya wani ya dade da wucewa kuma ba zai taba dawowa ba.

“Zan iya cewa, kimanin kaso 40 cikin 100 na marasa lafiyar da suke asibiti za su rayu ta hanyar kodar alade.

“Muna amfani da alade a matsayin abinci, yanzu kuma za mu rika amfani da shi a matsayin magani – alade yana da ma’ana a rayuwarmu.”

Ya ce, har yanzu binciken bai yi karfi ba, kuma ana bukatar a yi nazari a kai, “wannan ya ba mu wani sabon kwarin gwiwa kan wani gagarumin abu da za mu iya kai wa dakin bincike.”

Iyalan mutumin da aka dasawa kodar sun bayyana cewa, sun amin cewa wa masu tiyatar da su gudanar da wannan aiki.

Hukumar da ke lura da irin wadannan ayyuka ta Amurka ta amince a yi amfani da bangaren jikin aladen da aka jirkita halittarsa domin yin irin wannan bincike.

Wata likita da ke aiki a bangaren koda da kuma bangaren kulawar gaggawa ta Hukumar Lafiya ta Birtaniya (NHS) Dokta Maryam Khosrabi ta ce, sun dade suna nazartar yadda za a rika yin amfani da wasu sassan dabbobi a jikin dan Adam, amma jin dadinta a yanzu shi ne yadda wadannan likitocin suka nuna cewa, abu ne mai yiwuwa.

Kakakin sashin kula da jini da na dashe-dashe na hukumar NHS ya ce, yadda sassan dabbobi za su rika yi wa dan Adam daidai yanzu muka sa a gaba: “Ci gaba da wannan aikin dashen yau da kullum ya tabbata.