✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun tsawaita lokacin shiga yajin aiki da mako biyu

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa, NARD, ta dage lokacin shiga yajin aikin da ta yi shirin farawa da mako biyu domin bai wa Gwamnatin Tarayya…

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa, NARD, ta dage lokacin shiga yajin aikin da ta yi shirin farawa da mako biyu domin bai wa Gwamnatin Tarayya da ta jihohi damar warware matsalolin walwalar aikin mambobin kungiyar

Sanarwar tsawaita lokacin shiga yajin aikin na kunshe ne a wata takarda da kungiyar ta fitar bayan kammala taronta karo na 41 da ya gudana a Jihar Anambra.

Sanarwar ta ce kungiyar ta sha alwashin tsunduma yajin aiki gadan-gadan idan har ba a iya biya mata bukatunta ba yayin karewar wa’adin. 

A cewar kungiyar an dakatar da fara yajin akin ne biyo bayan alkawuran da gwamnatin ta yi a yarjejeniyar aiwatar aiki da aka sanya wa hannu a gaban Ministan Kwadago Dokta Chris Ngige, ranar 19 ga watan jiya.

Yayin taron da kungiyar Likitocin ta gudanar a Jihar Anambra