✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun ki yarda da rage albashi a Kaduna

Kungiyar Likitocin Najeriya ta yi watsi da kudurin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai na rage albashin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya na jihar da kashi…

Kungiyar Likitocin Najeriya ta yi watsi da kudurin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai na rage albashin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya na jihar da kashi 25 cikin 100, inda suka bukaci ya janye kudurin nashi domin kaucewa rikici.

Kungiyar ta bayyana rashin jindadinta game da kudurin gwamnati na rage albashin, a lokacin da gwamnatoci a fadin duniya suke karfafa wa ma’aikatan lafiya gwiwa ta hanyar inganta musu albashi da alawus-alawus.

“Kungiyar Likitocin Najeriya tana kira ga gwamnatin da ta gaggauta janye kudurinta domin ta kauce wa rikici a bangaren kiwon lafiya na jihar ta Kaduna kuma ta gaggauta mayar wa ma’aikatan kiwon lafiya da kashi 25 cikin 100 na albashinsu da aka yanke a watan Afrilu.”

Kungiyar ta kuma yi kira da “a inganta alawus-alawus din ma’aikatan lafiya kamar yadda aka cimma a matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin ma’aikatan.

Kungiyar likitocin ta kara da cewa zuwa yanzu sama da ma’aikatan lafiya 40 ne suka kamu da cutar coronavirus a yayin gudanar da aikinsu sannan da yawa suna fuskantar barazanar kamuwa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani sako da aka raba wa manema labarai wanda ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jihar, Dokta Stephen Akau Kache da sakataren kungiyar, Dokta Ifeanyi Aghadi Kene.

Kungiyar ta ce likitoci a Kaduna su ne koma-baya a albashi a fadin Najeriya inda ta jaddada cewa kungiyar ta janye yajin aikin da take yi na neman karin albashi ne saboda kishin kasa da kuma burin taimaka wa al’ummar jihar wurin dakile yaduwar cutar coronavirus.