✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci uku sun rasa rayukansu a Kano — NMA

Likitoci uku ne suka rasa rayukansu daga cikin 53 da suka harbu da cutar Coronavirus a Jihar Kano tun bayan barkewar annobar kamar yadda Shugaban…

Likitoci uku ne suka rasa rayukansu daga cikin 53 da suka harbu da cutar Coronavirus a Jihar Kano tun bayan barkewar annobar kamar yadda Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar, Dokta Usman Ali ya bayyana.

A zantarwarsa da manema labarai, Dokta Usman ya ce mutuwar da aka samu a bayan nan ta wani kwararren likitan yaki da cututtuka wanda ajali ya katse masa hanzari a cibiyar killace masu dauke da cutar Coronavirus a ranar Litinin ta makon jiya.

A yayin da wasu daga cikin ’ya’yan kungiyar likitoci ke kamuwa da cutar kuma adadin yake ci gaba da hauhawa, Dokta Usman ya ce alkaluman wadanda su kamu sun hada ne da wadanda suka kamu a zagayen annobar na farko da na biyu.

Ya ce, “A yanzu haka muna da likitoci 53 da aka tabbatar sun kamu da cutar kuma uku daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya a nan Kano.”

“Daya daga cikin likitocin da suka mutu a baya-bayan nan wani kwararren likitan yaki da cututtuka ne wanda yam utu a cibiyar killace wanda suka kamu da cutar,” inji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin da guguwar annobar coronavirus ta sake kadawa a duk fadin duniya, an samu akalla likitoci 20 da suka mutu a fadin Najeriya cikin mako daya a karshen watan Dasumbar bara.

Kungiyar Likitocin Najeriya NMA reshen birnin Abuja ce ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar ta bakin Shugabanta, Dokta Enema Amodu.