✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci za su yi wa Putin aikin cutar daji

Ana sa ran Putin zai mika ragamar mulki Rasha ga wani na hannun damansa, Cif Nikolai Patrushev.

Likitoci za su yi wa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin aiki kan cutar daji da ke damunsa kamar yadda majiyoyi daga kasar suka bayyana.

Bayanai sun ce idan shugaba Putin ya tafi kwanta jinya, na hannun damansa Cif Nikolai Patrushev ne, zai ci gaba da jagorancin kasar.

Duk da dai cewar sunan Patrushev bai shahara ba a duniya, amma yana cikin ‘yan gaban goshin Putin kuma daya daga cikin wanda suka kitsa mamayar da aka yi wa Ukraine.

Rahotanni sun bayyana Patrushev ya taka muhimmiyar rawa wajen kai hare-hare kan Ukraine.

Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da yanayin rashin lafiyar Putin ke bayyana ga duniya ba.

Wata majiya ta shaida cewar kusan shekara daya da rabi ke nan shugaban na fadi-tashi da cutar dajin.

Ana sa ran shugaban na Rasha zai tafi neman lafiyarsa inda za a yi masa aiki.

Bayanai sun nuna Putin zai dauki lokaci ba tare da jan ragamar shugabancin kasar ba, amma ba lallai ne kowa ya fuskanci hakan ba sakamakon na hannun damansa zai kula da komai.

Rahotanni sun bayyana cewar rashin lafiyar Putin ba ta yi tsananin ba, amma akwai bukatar yi masa aiki don gudun kada ta ta’azzara.