✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Limamin cocin da ya ce ya san ranar da Annabi Isah zai bayyana wakilin Shaidan ne – CAN

Kungiyar ta ce babu wanda ya san ranar sai Allah

Kungiyar Mabiya Addinin Kirista ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Ondo ta tsame kanta daga ikirarin sanin ainihin ranar da Annabi Isah (A.S) zai dawo doron kasa da wani Limamin Coci a Jihar ya yi.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Pastor Bayo Oladeji na kungiyar ya sanya wa hannu.

Ya ce Limamin Cocin Whole Bible Believers da ke garin Ondo Pastor Josiah Peter Asumosa wanda ya yi ikirarin cewa Annabi Isah zai dawo doron kasa a cikin watan Satumba mai zuwa ya fadi hakan ne domin yaudarar mutane 77 da suka amince aka boye su cikin wani wuri a karkashin kasa a cikin cocin domin jiran ganin wannan rana.

Ikirarin farko da Limamin Cocin ya yi ya bayyana cewa Yesu Almasihu zai dawo ne a ranar 22 ga watan Afrilu da ya gabata.

“Babu Limamin Cocin da zai ce ya san ainihin ranar da Yesu Almasihu zai dawo doron kasa domin littafin Bible ya fayyace gaskiyar cewa Allah kadai ne ya san wannan rana.

“Duk wanda ya ce ya san wannan rana yana zolayar jama’a ne kuma wakilin Shaidan ne,” inji CAN.

Kungiyar ta kuma ta yi kira ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Ondo da ta gudanar da binciken kwakwaf domin gano wannan Limamin da ainihin cocin nasa domin hukunta shi.

CAN wacce ta ce ba ta san da zaman wannan Faston da cocinsa ba ta yi kira ga mahukunta a Jihar Ondo da su yi kyakkyawan aikin duba lafiyar mutane 77 da suka shafe wata shida suna boye suna jiran dawowar Yesu.