✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lionel Messi: Gwagwarmayar shekara 20 a Barcelona ina aka dosa

A ’yan kwanakin baya ne dan asalin kasar Argentina kuma kyaftin dinta wanda yake taka leda a Barcelona na tsawon lokaci Lionel Messi dan shekara…

A ’yan kwanakin baya ne dan asalin kasar Argentina kuma kyaftin dinta wanda yake taka leda a Barcelona na tsawon lokaci Lionel Messi dan shekara 33, ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga kungiyar inda ya aike mata sakon kar ta kwana.

Hakan baya rasa nasaba da irin dambarwar da ke tsakaninsa da hukumomin kungiyar, wanda ya janyo manyan kungiyoyi a fadin Nahiyar Turai suke bayyana kwadayinsu na sayen dan wasan muddin suka warware dambarwar da ke tsakaninsa da Barcelona.

Kungiyoyi irin su Manchester City da PSG da Inter Milan sun nuna kwadayin sayen dan wasan, wanda komai ka iya faruwa.

Dan wasan ya shafe shekara 20 da zuwa kungiyar ya kuma kai 17 da fara taka leda a bana.

Nasarorin da ya samu

Lionel Messi dan shekara 33 daya ne daga cikin wadanda suka fi kowa hazaka a fagen taka leda, wanda ake yi wa kallon ya fi duk wani mai buga kwallon kafa iya murza leda a duniya.

Messi ya kasance wanda ya fi kowa zura kwallo a kakar wasa ta 2007/2008 a gasar La-Ligar kasar Sifaniya.

Sannan dan wasan ya kafa sabon tarihi na zama wanda ya fi taimakawa wajen zira kwallaye a kakar wasa daya tilo.

Messi ya fi duk wani dan kwallo a tarihi wanda ya lashe kyautar (Ballon d’Or awards) wanda hakan tasa ya zama dan kwallon da ya fi kowa iyawa a duniya, inda ya lashe kyautar har sau 6, wanda Cristiano Ronaldo yake bi masa da kyauta 5.

Shi ne dan wasan da ya fi kowanne dan wasa a Barcelona yawan cin kwallaye a tarihi inda ya zira kwallo 634 a fafatawa 731 da ya yi.

Shi ne kuma wanda ya fi samun nasarar zira kwallaye a gasar La Liga da kwallo 444 a wasa 485 da ya fafata.

Gwarzon dan wasan ya yi wata bajinta a shekarar 2012 inda ya zira kwallaye 91 a wasannin da ya fafata wa Barcelona da kasarsa ta Argentina a wasanni 69 da ya buga.

Ya samu nasarar lashe kofuna 34, ya lashe gasar La Liga sau 10 sai kuma ya lashe kofin zakarun Turai guda 4.

Wani abin bajintar kuma shi ne wanda ya fi kowa zura kwallaye a kasarsa ta Argentina inda yake da kwallo 70 a wasa 138 da ya buga.

Tsohon dan wasan Barcelona Gary Lineker ya ce, “shi ne dan wasan da ya fi kowa fice a fagen murza leda”.

Shi ne dan wasa na farko da ya fara zura kwallo sama da 20 tare da taimakawa a zira sama da 20 a gasar La-Liga a kakar wasa daya.

Sai tsohon dan wasan Arsenal Thierry Henry wanda ya zira kwallaye 24 kuma ya taimaka aka ci 20 a kakar wasa ta 2002/ 2003 a kasar Ingila.

Shin tauraruwar dan wasan ta fara dusashewa?

Wani dan jarida mai sharhi a kan wasannin La Liga wanda ta kai shi ga rubuta littafi a kan Messi, ya bayyana Messi da cewa: “Messi a yanzu baya kan ganiyarsa kamar yadda aka san shi, sai dai hazakar da ya nuna a kakar wasa ta bara ta nuna cewa har yanzu shi ne dan wasan gaba da ya fi kowa hazaka a duniya”, inji shi.

Sai dai a bangaren zura kwallaye zancen ya canza inda a halin yanzu an sha gabansa.

Messi ya lashe kyautar (Pichichi ‘golden boot’) ta La Liga (kyautar takalmin zinare) sau 7 wanda ya lashe sau 4 a jere, sai dan wasan Real Madrid Karim Benzema da ke bi masa baya sau 4.

Duba da cewa kungiyar Barcelona a wannan karon ba ta lashe komai ba, wanda rabonta da ta samu irin wannan rashin nasara tun kakar wasa ta 2013/2014.

A wannan karon ne aka samu dan wasan da ya ci kasa da kwallaye 30 a matsayinsa na wanda ya fi zira kwallaye tun dan wasan Deportivo, Diego Tristan a kakar wasa ta 2001 zuwa 2002 wanda shi ne ya zira kwallo kasa da na Messi a kakar bana.

Messi ya karya tarihin Davi a bangaren taimakawa wajen zura kwallaye.

An fi shi zura kwallo a bana

Dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski, a bana ya zira kwallaye 55, sai dan wansan SS Lazio Ciro Immobile da kwallo 36, da Cristiano Ronaldo na Juventus da kwallo 31 sai Romelu Lukaku na Inter Milan da kwallo 23 sai dan wasan RB Leipzig Timo Werner, wanda ya koma Chelsea.

Duk sun zura wa kungiyoyinsu kwallaye sama da wanda Messi ya zira.

Kazalika Raheem Sterling na Manchester City ya zira kwallo 31 a bana.

Amma idan aka zo bangaren agazawa a zira kwallo Messi ne kan gaba idan haka hada da kwallo da taimakawa a zira yana da jimillar 56.

Lewandowski shi kadai ke gaba da Messi idan aka kwatanta hazaka, wanda ake tunanin zai iya lashe kyautar Ballon d’Or idan za a bayar a bana, duba da yadda annobar coronavirus ta kawo cikas ga harkar wasanni.

Bangaren yanka wato (dribbles) Adama Traore ya samu nasarar yanka har sau 275 wanda ya zarce na Messi mai 260 fadin Nahiyar Turai.

 Ya za a kwatanta Messi a da da yanzu

Idan za a kwatanta Messi a da, da yanzu babu wani canji a bangaren tabe-tabe da bayar da kwallo (passing) da yanka (dribbles) da kuma kirkirar damar zira kwallo.

Wajen da ake ganin ya samu nakasu shi ne wajen buga kwallo daga nesa wato (shooting).

Daga cikin bayanan Messi da aka adana a kakar wasa ta 2008/2009 a lokacin da ya fara zira kwallo 20 da kuma irin hazakar da ya nuna a lokacin, an samu nakasu idan aka kwatanta da bayanan da aka tattara na wasannin da Barcelona ta buga a kakar wasa ta bana.

Messi yana daukar minti 126 kafin ya zira kwallo daya a raga wanda idan aka kwatanta da kakar wasa 11 da suka gabata, ya samu koma baya.

Bangaren yanka kuma (dribbles) dan wasan ya rike matsayinsa na baya sai dai har yanzu yana da kaso 65 cikin dari ne kawai.

A bangaren bayar da kwallo kuma (passing) yana da kashi 85 cikin 100 za a iya cewa ya samu koma baya duba da yadda dan wasan yake a kakar wasa ta 2009 zuwa 2010.

Shin yana sauya waje (position) a cikin fili?

Messi ya soma buga kwallo a bangaren dama, sai dai banagren da ya fi nutsawa shi ne tsakiyar fili.

Masu bibiyar dan wasan sun yi kididdigar wajen da dan wasan ya fi tsayawa a wasannin da yake bugawa na gasar La-Liga.

A kakar wasa ta bara da yawa daga cikin kwallon da yake bayarwa suna zuwa ne daga tsakiyar fili wato bayan lamba 9 sannan yana biyowa ta vangaren dama.

A cewar West, “Messi ya rasa wasu damarmaki a cikin fili inda yake yi masa wahala ya yanke masu tsaron baya a cikin yadi na 20,” inji shi.

Sai dai kuma har yanzu yana da hanzarin da aka san shi da shi a lokacin da ya yi gaba da gaba da masu tsaron baya.

A kakar wasa ta bara Messi ya buga wasa a gaba wajen zira kwallo, kafin daga baya adawo da shi tsakiyar fili a matsayinsa na mai kirkirar dama.

Wannan sauyi na wajen tsayawar Messi ya zama dole duba da babu wani dan wasa da zai iya buga matakan da zai buga daban-daban, amma a yanzu ana ganin cewa Messi zai kammala wasansa ne a matsayin lamba 10.

Lamaba 10 ita ce lamabar da dan wasa yake samun damarmaki ba tare da wahalar da kai ba, wanda har yanzu ba a samu wanda yake bayar da kwallo da yanka da bugu daga nesa ba kamar Messi a Barcelona.

An tambayi mai horar da Manchester City game da Messi za a iya hada shi da dan wasansa Sergio Aguero, sai ya ka da baki ya ce Messi shi ne ya fi kowanne lamba 9 hazaka.

Pep Guardiola ya ce, “Messi shi ne gaba da kowa, Messi shi ne lamba 9 shi ne lamaba10 da 11 da 6 da 5 da 4….”.

Shin har yanzu Messi shi ne kan gaba a wajen murza leda a duniya?

Har yanzu akwai zazzafar muhawara game da ko Messi ne ya fi kowa hazaka a duniya a halin yanzu ko akasin haka.

Kodayake dan wasan Bayern Munich Lewandowski, ya nuna bajinta a kakar wasa da ta gabata sama da duk wani dan wasa.

Ya kasance daya daga ciki zakakuran masu zura kwallo a duniya da kuma iya yanka da bayar da kwallo ga abokan wasa wanda ake hasashen idan yana manayan kungiyoyi sai ya fi haka hazaka.

Lewandowski ya kasance daya daga cikin wadanda suka wargaza wa Barcelona lissafi inda suka lallasa su da ci 8 da 2 wanda ake tunanin abin da ya kawo karshen wasan Messi a Barcelona ke nan.

Messi ya ci kyautar takalmin zinare sannan shi ne kan gaba wajen wadanda suka taimaka aka zura kwallo a raga, wanda ya nuna cewa har gobe zai zama kadara ga kowace kungiyar da za ta saye shi.

Abin da ake tunani kadai zai iya kawo masa cikas shi ne lokaci, kodayake tsohon abokin wasansa a Barcelona Davi ya taba bayyana cewa yana tsammani Messi zai iya kaiwa shekara 40 yana murza leda.

Tsohon dan wasan Barcelona Lineker ya ce: “Ba karamar alfarma ba ce ka dinga kallon Messi a cikin fili yana fafata wasa, hakazalika zai zama abin bakin ciki a lokacin da kake kallon wasan Messi na karshe.

“Babu wani dan kwallon da zai yi karko har abada. A yanzu haka kana iya fahimatar karfin Messi yana raguwa. Duka yadda ka kai da iya wasa ba za ka wuce lokacinka ba”, inji shi.

West ya ce, “Messi har yanzu shi ne kan gaba zuwa nan da dan lokaci”.

Abin jira a gani kadai shi ne dan shekara 33 zai kai kimanin farashin nawa a fagen cinikayya a kakar wasa ta bana koma wacce kungiya ce za ta samu damar sayen sa; Sannan wane irin sauyi zai kawo a duk gasar da ya koma.

Lokaci dai kadai shi ne al’kali.