Liverpool da Bayern Munich sun cimma matsaya kan cinikayyar Mane | Aminiya

Liverpool da Bayern Munich sun cimma matsaya kan cinikayyar Mane

    Abubakar Muhammad Usman

Dan wasan gaban Liverpool, Sadio Mane na gab da komawa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke kasar Jamus.

Tuni dan wasan ya kammala kulla yarjejeniyar tsakaninsa da kungiyar kan sanya mata hannu na tsawon shekara uku.

Bayern Munich za ta biya kudi Yuro miliyan 32 ga Liverpool don daukar dan wasan gaban.

Kazalika, Liverpool za ta karbi Yuro miliyan 40 daga hannun Bayern Munich a matsayin kafin alkalami.

Sadio Mane, wanda dan asalin kasar Senegal ne, ya bayyana wa Liverpool aniyarsa ta barin kungiyar tun bayan kammala wasan karshe na gasar zakarun turai da suka yi rashin nasara a hannun Real Madrid da ci daya mai ban haushi.

Ana sa ran kungiyoyin biyu za su cimma matsaya a ranar Juma’a don kammala cike-ciken takardun sayar da Mane.