Liverpool na son sayar da Takumi Minamino | Aminiya

Liverpool na son sayar da Takumi Minamino

    Abubakar Maccido Maradun

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta amince za ta sayar da dan wasanta na tsakiya, Takumi Minamino, ga Monaco da ke kasar Faransa a kan kudi Yuro miliyan 18, kwatankwacin Fam miliyan 15.5.

Kungiyar kwallon kafar da ke kasar Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan mai shekaru 27 da haihuwa, kuma dan asalin kasar Japan.

Takumi, wanda ke taka wa Liverpool leda tun a shekarar 2020 bayan ya bar tsohuwar kungiyarsa ta Red Bull Salzburg a kan kudi Fam miliyan bakawai da dubu 200.

Shi dai dan wasan ya ci wa Liverpool kwallo har sau 14 a cikin wasanni 55 da ya buga mata.

Kazalika, shi ne dan wasa wanda ya fi kowane zura kwallo a raga a kananan gasar da kungiyar ta buga a kakar bara.