✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Liverpool ta je har gida ta lallasa Inter Milan da ci 2

Liverpool ta hada wa Inter Milan jikinta a gaban magoya bayanta.

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta je har gidan Inter Milan ta doke ta da ci biyu a gaban magoya bayanta a Gasar Zakarun Turai.

Wasan da kungiyoyin biyu suka buga a matakin ’yan 16, an yi dauki-ba-dadi kafin daga bisani Liverpool ta samu nasarar jefa kwallaye biyu.

An shafe kashin farko ma wasan ba tare da kowa ya zura kwallo a ragar abokiyar hammayarsa ba; Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Liverpool ta fara zura kwallo ta farko.

Dan wasan gaban Liverpool, Robert Firmino, ne ya fara jefa kwallo a minti na 75, kafin daga bisani Mohamed Salah ya jefa ta biyu a minti na 83.

Yanzu haka dai kafar Inter Milan daya na waje daya kuma na cikin gasar, har zuwa lokacin da za su sake karawa a karo na biyu a filin wasan Liverpool, wato Anfield.