✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Liverpool ta tsallaka zuwa Wasan Karshe na Gasar Zakarun Turai

Tunda ta yi kasa-kasa da Villarreal, Liverpool za ta fafata da duk wanda ya yi nasara tsakanin Real Madrid su Manchester City

Liverpool ta samu nasarar zuwa sawan karshe na Gasar Zakarun Turai bayan lallasa kungiyar kwallon kafa ta Villarreal da ci 3-2 har gida.

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta samu wannan nasara ne bayan yin hobbasa daga ci 2 babu ko daya da Villarreal ta yi mata kafin tafiya hutun rabi lokaci.

Jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Liverpool ta warware kwallayen baki daya tare da kara wata a kai, wanda hakan ya ba ta nasarar samun tikitin zuwa wasan karshe na gasar.

Da farko dai Villarreal ta zura kwallo a minti na uku da fara wasan ta hannun dan wasanta Boulaye Dia, yayin da Francis Coquelin ya kara a minti na 41.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Liverpool ta yi wasan kura da Villarreal, inda ’yan wasanta Fabinho, Luis Diaz da Sadio Mane suka jefa mata kwallaye a minti na 62 da 67 da kuma minti na 74.

Dama tuni Liverpool ta samu nasarar doke Villarreal da ci 2 babu ko daya a zagayen farko na wasan da aka doka a filin wasa na Anfield da ke kasar Birtaniya.

Kungiyar ta samu nasara da jimullar kwallaye 5 da 2 ke nan, wanda yanzu haka za ta jira kungiyar da za ta barje gumi da ita a wasan karshe na gasar tsakanin Real Madrid ko Manchester City, wadanda za su fafata a daren ranar Laraba.