✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool ta yi wa Villarreal wankan jego da ci 2-0

Liverpool na dab da samun tikitin zuwa wasan karshe na Gasar Zakarun Turai.

Liverpool ta karbi bakuncin Villarreal a Gasar Zakarun Turai, inda ta ragargaje ta da ci 2 babu ko daya.

Liverpool ta yi kane-kane tun a mintin farko na wasan, inda ta dinga yi wa Villarreal ruwan hare-hare.

An shafe kashin farko na wasan ba tare da an zura wa kowace kungiya kwallo a raga ba, har aka tafi hutun rabin lokaci babu ci.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dan wasan bayan Villarreal, Estupinan ya yi rashin sa’a wajen zura kwallo a ragar kungiyarsa a minti na 53.

A minti na 55 ne dan wasan gaban Liverpool Sadio Mane ya sake zura mata kwallo.

Liverpool ta kai hare-hare har guda 20 a wasan, inda guda 15 daga ciki suka yi fadi, sai guda biyar da suka zama masu hatsari.

Ita kuwa Villarreal hari daya ta kai kacal, kuma shi ma ya yi fadi.