Lokaci ya yi da Buhari zai saka wa Tinubu —Kashim Shettima | Aminiya

Lokaci ya yi da Buhari zai saka wa Tinubu —Kashim Shettima

Sanata Kashim Shettima
Sanata Kashim Shettima
    Muhammad Aminu Ahmad

Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a saka wa Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Aswaju Bola Ahmed Tinubu, kan hidimar da ya yi wa jam’iyyar.

Sanata Shettima wanda ya jagoranci taron masu goyon bayan takarar neman shugabancin Tinubu, ya ce babu wanda ya fi cancanta ya kasance Shugaban Kasa a badi kamar Tinubu.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar Shugaban Kasa a farkon makon jiya.

Magoya bayansa sun bayyana cewa kamata ya yi Shugaba Buhari ya ba da tasa gudunmawar don ganin Tinubu ya samu nasara, lura da irin rawar da ya taka wajen samun nasarar Jam’iyyar APC a zaben 2015.

Sanata Shettima ya kara da cewa don wanzar da gaskiya da kuma adalci, ya kamata Jam’iyyar APC ta tura tikitin takarar Shugaban Kasa ga shiyyar Kudu, kuma ta bayar da takarar ga Bola Tinubu.

A shekarar 2015 akwai ’yan takarar da suka rika bugun kirji don ganin sai jam’iyyar ta ba su takara, amma Tinubu ya tsaya kai-da-fata ya nuna goyon bayansa ga takarar Shugaba Buhari.