✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Sakkwato: Lokacin kawo karshen ’yan bindiga ya yi — Buhari

Buhari ya ce babu sauran inda 'yan bindiga za su buya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin kawo karshen ’yan bindiga da suke addabar wasu yankuna na kasar nan.

Ya yi gargadin ne ranar Litinin bayan kisan sama da mutum 60 da wasu ’yan bindiga suka yi  a wata kasuwa da ke Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.

Shubaban, ta hannun hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu, ya ce kwanakin ’yan bindigar ya zo karshe.

Ya ce an bawa rundunar soji kayan aikin da suka dace don yakar ta’addancin da ake fama da shi a wasu yankuna na kasar nan.

Ya roki ’yan Najeriya cewar “Kar ku fitar da rai saboda wannan gwamnati ta shirya fiye da kowanne lokaci wajen kare rayukan ’yan Najeriya daga ’yan ta’adda wanda ba su tausayi bare imani.”

Har wa yau, shugaban ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wanda suka rasa rayukansu a harin na Goronyo, inda ya ce jama’a su yi hakuri saboda rundunar soji na fito da sabbin dabarun yaki.

“Lokacinku ya zo karshe saboda babu sauran inda za ku ci gaba da buya.

“’Yan bindiga na cikin wani hali a yanzu saboda ruwan wuta ta sama da kasa da suke sha daga jami’an tsaronmu.

“Amma su sani yanzu babu sauran wani waje da za su buya ba tare da dakarunmu sun bankado su ba,” cewar shugaba Buhari.