✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lokuta hudu da Rahama Sadau ta jawo cece-kuce a Kannywood

Jarumar ta kasance daya daga cikin jarumai masu yawan jawo cece-kuce a masana’antar.

Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau jaruma ce wadda ta gwanance a wajen shirin fim, inda har ta kai ta fara shirya fim nata, kamar shirin Rariya, wanda ya yi fice sosai.

Sai dai duk da kwarewarta a fim, jarumar ta kasance daya daga cikin jarumai masu yawan jawo cece-kuce a masana’antar.

Hakan ya sa Aminiya ta yi tariya, inda ta rairayo lokuta hudu da jarumar ta jawo cece-kuce:

Rikici tsakaninta da Adam A. Zango

A shekarar 2015 ce jarumar ta fito fili ta wallafa a shafinta na Instagram cewa jaruma Adam A. Zango ya cire ta ne a fim dinsa mai suna Duniya Makaranta saboda ta ki amincewa da shi.

A lokacin ta yi rubutu mai zafi tare da amfani da munanan kalamai a kan jarumin wanda hakan ya jawo cece-kuce sosai da rigima, domin a lokacin ta nuna cewa ba ta bukatarsa, domin tana da Ali Nuhu.

Hakan ya jefo Ali Nuhu cikin rigimar yayin da daga bisani ta goge rubutun, sannan ta ba shi hakuri.

Waka da Classiq

A shekarar 2016 kuma aka ga wani bidiyon waka, inda aka ga jarumar suna waka tare da mawakin Turanci, Classiq, inda ya rika rike ta.

Bidiyon ya jawo maganganu, inda aka rika cewa hakan ya saba da addinin Musulunci da al’adar Bahaushe.

Saboda bidiyon ne a ranar 26 ga Oktoba na shekarar 2016, Kungiyar MOPPAN ta dakatar da jarumar daga harkokin fim baki daya.

Daga baya ta nemi afuwa, sannan Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano, karkashin Isma’ila Na’abba Afakallah ta yafe mata.

Murnar bikin haihuwarta da bude wajen hutu na Sadauz Home

A shekarar 2019 kuma, jarumar ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta tare da bude katafaren wajen hutu a Kaduna.

Wannan wajen hutu, wanda ke kan Titin Rabah a Unguwar Sarki a Kaduna ya kunshi wajen cin abinci da na wanke kai na mata da wajen aski da wajen shan shisha da sauransu.

Bikin bude wajen ya zo ne kwanakin kadan bayan bikin murnar cikarta shekara 26, wanda bikin ya jawo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, musamman batun bude wajen shan shisha da suturar da ta sanya a wajen bikin.

A nan ma ta saka wasu hotuna da ke nuna sassan jikinta tare da mawaki Classiq suna tikar rawa, wanda hakan ya jawo cece-kuce matuka.

A wannan lokacin, wasu jarumai sun nesanta da kansu, tare da yin tir da abin da ta yi.

Sanya hotuna masu nuna jiki

A bana kuma, jarumar ta jawo cece-kucen da ya fi kowanne zafi, bayan ta saki wasu hotuna da suka nuna jikinta, inda a kasan hotun wani ya yi batanci ga Manzon Allah, sannan kuma aka ci mutuncin Musulunci.

Wannan karon lamarin ya fi zafi ne, musamman ganin yadda kusan duk masana’antar Kannywood suka nesanta kansu da ita, inda wasu ma har tsinuwa suka yi.

Tuni ta nemi afuwar mutane, inda ta ce ita Musulma ce, kuma ba za ta so a batanci ga Manzon Allah da addinin Musulunci ba.

Amma duk da haka, Kungiyar MOPPAN ta sake dakatar da ita daga harkokin fim, inda ta ce dama a ko a wancan lokacin, ba ta yafe mata ba.