✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

LP da PDP sun lashe kananan hukumomi 2 a zaben shugaban Kasa a Kaduna 

Jam'iyyar LP da ta PDP kowannensu ya lashe kananan hukumomi biyu a Jihar Kaduna kamar yadda hukumar zabe ta bayyana.

Jam’iyyar LP da ta PDP kowannensu ya lashe kananan hukumomi biyu a Jihar Kaduna kamar yadda hukumar zabe ta bayyana.

Sakamakon zaben ya nuna PDP ce ta lashe Karamar Hukumar Giwa da
Kuriu 22,302 sai APC ta samu kuri’u 19,922 LP kuri’u 565 sai
NNPP da kuri’u 3,114.

A karamar hukumar Makarfi kuwa
APC ta samu kuri’u 13,767,
PDP ta samu 22,098 sai LP ta samu kuri’u 759, NNPP kuwa kuri’u 5,219 ta samu.

Ita kuwa jamiyyar LP ce ta lashe zabukan da aka yi a Karamar Hukumar Kaura da kuri’u 25,744 sai
APC mai kuri’u 1,847, ita kuwa PDP ta samu kuri’u 7,847 sai NNPP Mai kuri’u 320

A Kajuru APC ta samu kuri’u 3,940 sai PDP mai kuri’u 9,253 da
LP mai kuri’u14,875 sai
NNPP ta samu kuri’u 1,221.