✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Luiz Lula ya sake zama Shugaban Brazil bayan fitowa daga gidan yari

Lula ya doke shugaba mai ci bayan lashe kashi 50.9 na adadin kuri’un da aka kada a zaben.

Tsohon Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya doke shugaba mai ci Jair Bolsonaro a zaben Shugaban Kasa bayan fitowarsa daga gidan yari.

An daure tsohon shugaban ne a gidan yari bayan da wata kotu ta same shi da laifin karbar cin hanci daga wani kamfanin gine-gine don ya ba shi kwangila a kamfanin Mai na Petrobras mallakin gwamnatin Kasar.

Kafin yanzu dai Lula wanda ya shafe kwanaki 580 a gidan yari, an haramta masa tsayawa ko wacce irin takarar siyasa a kasar har ya mutu.

Sai dai Lula ya samu kansa ne bayan da wata babbar kotu ta soke hukuncin wanda hakan ta sake ba shi damar komawa siyasa, sannan ya kuma sake tsayawa takarar shugaban kasar har ya yi nasara.

“Sun yi kokarin binne ni da raina, sai kuma ga shi na dawo (ban mutu ba),” in ji Lula a jawabinsa na murnar lashe zaben.

Lula ya doke shugaba mai ci Jair Bolsonaro bayan lashe kashi 50.9 na adadin kuri’un da aka kada a zaben.