✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikacin lafiya ya sake kamuwa da COVID-19 bayan an yi masa rigakafi

Ma'aikacin ya sake harbuwa da COVID-19 kwanaki hudu bayan karbar rigakafin cutar.

Daya daga cikin ma’aikatan lafiya dake aiki a Cibiyar Agajin Gaggawa ta Amurka ya kamu da Korona bayan an masa rigakafin maganin kamfanin Pzifer.

An dai yi wa ma’aikacin mai suna Matthew W. rigakafin kamfanin Pfizer da BioNTech, a ranar 18 ga Disambar 2020, inda a lokacin ya ce ba ya ji wani ciyo face na hannu.

Sai dai kafofin yada labarai dake kasar ta Amurka, sun bayyana cewa ya nuna wasu alamun cutar kwanaki shida bayan yi masa rigakafin.

Bayan masa gwaji kuma, sakamakon ya nuna yana dauke da cutar.

To sai dai masana bincike sun ce ba abun mamaki bane saboda bai nuna alamun da ake so ba lokacin da ya karbi rigakafin.

Wani likita dake Cibiyar Dakile Cututtuka ta San Diego a Amurka, Christian Ramers, ya ce ya kan dauki tsawon kwanaki 10 zuwa 14 kafin maganin ya fara aiki a jikin mutum.