Ma’aikata 774,000: Keyamo ya koma gefe kawai | Aminiya

Ma’aikata 774,000: Keyamo ya koma gefe kawai

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan

Majalisar Dattawa ta bukaci Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo da ya cire hannunsa daga shirin Gwamnatin Tarayya na daukar kananan ma’aikata 774,000 a kananan hukumomi.

Majalisar ta ce babu ruwan ministan da aiwatar da shirin wanda aiki ne da ya kebanci Hukumar Samar da Ayyuka ta NDE. Don haka ta bukaci Keyamo wanda a baya suka yi cacar baki da shi kan batun, da ya tsaya a matsayinsa na mai sa kula da aikin NDE, wadda ke karkashin ma’aikatarsa.

“NDE ce mai alhakin gudanar da Naira biliyan 52 da aka ware wa shirin na ma’aikata 774,000, saboda haka wajibi ne a gudanar da kudaden yadda ya kamata, ita kuma Ma’aikatar Kwadago ta Kyautatuwar Ayyuka ta tsaya a matsayinta na mai lura”, inji Majalisar.

Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan ya ce Majalisar na kan bakanta cewa NDE ce ke da wuka da nama a daukar ma’aikatan, “aikin ma’aikatar shi ne lura da yadda za a yi shi, ita kuma Majalisar Tarayya aikinta shi ne sa ido”.

Ahmad Lawan ya ba da tabbaci cewa Majalisa za da sa ido sosai a kan shirin domin ‘yan Najeriya su ci moriyarsa.