✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata 774,000: Majalisa ta yi zaman gaggawa

Majalisar Dattawa ta kira taron gaggawa kan matakin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000 a Najeriya. Hakan ya faru ne bayan…

Majalisar Dattawa ta kira taron gaggawa kan matakin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000 a Najeriya.

Hakan ya faru ne bayan umarnin yin daukar ma’akatan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa minista a ma’aikatar, Festus Keyamo, a ranar Talata baya majalisar ta dakatar da shirin.

Da yake magana da manema labarai, Keyamo ya ce Shugaba Buhari ya ba shi damar ci gaba da shirin ba tare da la’akari da matsayar Majalisar Tarayya ba a kan lamarin.

Keyamo da ‘yan majalisar sun kai ruwa rana kan zargin da ya yi musu na neman yin babakeren a shirin na daukar ma’aikatan.

Su kuma ‘yan majalisar suka zarge shi da yin gaban kansa a shirin na Hukumar Daukar Ma’aikata ta Kasa (NDE).

Hakan ya kai su ga cacar bakin da ya sa majalisar ta tsayar da shirin a makon jiya.