✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata sun rufe tashoshin jirgin kasa, sun fara yajin aiki

Ma'aikata na neman karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.

An rufe tashoshin jirgin kasa a fadin Najeriya bayan ma’aikatan Hukumar Sufurin Jiragen Kasa sun fara yajin aiki.

Tun a cikin dare kafin wayewar garin Alhamis ne ma’aikaran suka rufe tashoshin jiragen kasan domin fara yajin aikin da suka shirya na kwana uku.

Ma’aitan sun tsunduma yajin aikin gargadin ne domin neman a yi musu karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.

A ranar Asabar, Ministan Sufurin Jiragen Kasa, Rotimi Amaechi, ya yi wata tattaunawa da shugaban kwadago daga cikin ma’aikatan, domin shawo kan matsalar, amma aka tashi ba tare da cim ma daidaito ba.

Daga baya ministan ya sake kira wani zama da su, nan ma haka ba ta cim ma ruwa ba.