✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Landan

Sun koka cewa rabon da a yi musu karin albashi tun 2012

Dubban yan kwadago sun yi tattaki zuwa Majalisar Dokokin Birtaniya domin kokawa kan tsadar rayuwa da rashin kyakkyawan albashin da suke fama da shi a kasar.

Kungiyar Kwadagon Kasar ta TUC ce dai ta shirya zanga-zangar, inda ta yi kira ga gwamnatin da ta kara mafi karancin albashi a kasar zuwa Euro 15.

To sai dai Kakakin Sashen Kudi na gwamnatin kasar ya ce gwamnatin na nan na kokarin lalubo hanyar da za ta samarwa ma’aikatan sauki daga halin da suke ciki.

Haka kuma, ya ce ko a yanzu gwamnatin na taimaka wa mutane kusan miliyan takwas a bana da Yuro 1,200 ta tsarin biyan kudi na kai tsaye, tare da tallafa wa kowanne gida da Yuro 400 domin biyan kudin makamashi.

Kungiyar kwadagon dai ta ce bincikenta ya gano mata cewa hauhawar farashin kaya ya sanya ma’aikata asarar kimanin Yuro 20,000 tun daga shekara ta 2018, yayin da albashinsu ya gaza motsawa daga inda yake tun shekara ta 2012.

Babban Sakataren kungiyar, Frances O’Grady ya shaida wa BBC cewa  hakurin ma’aikatan ya kare  kan rashin karin albashi har tsawon shekara 10, domin ba su ne suka haifar da hauhawar farashin ba, hasalima akansu yake karewa.

Shi ma dai wani ma’aikaci mai suna Ben Robinson mai shekaru 25 wanda ke cikin ma’aikatan da  suka gudanar da zanga-zangar, kuma ya ce wani ma’aikacin a yanzu na da zabin  hakura da ciyar da kansa ya ciyar da iyalansa, ko kuma su hakura don ya samu ya biya kudin haya.

A nata bangaren gwamnatin kasar Birtaniyar ta ce: “A wani bangare na kunshin tallafin Yuro biliyan 37 na gwamnati, mu na kokarin tallafar kananan ma’aikata da fiye da Yuro 330 a shekara, ta hanyar rage harajin Inshorar kasa, domin masu neman lamuni na duniya su ci gaba da samun karin £1,000 wanda kaso ne mafi girma daga abin da suke samu, kuma suka rage kaso mafi girma da aka taba samu ga harajin mai”.