✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan da muka samu da sakaci babu su a zaben gwamna —INEC

Dole mu kara kokari kan abin da muka yi a Zaben Shugaban Kasa.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta dakatar da dukkan ma’aikatan da aka samu da sakaci lokacin zaben Shugaban Kasa da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, 25 ga watan Fabirairu.

INEC ta ce dukkansu ba za su yi aikin zaben da za a yi ba na ’yan majalisar jiha da na gwamnonin a kasar da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kwamishinonin Zabe a ranar Asabar a Abuja.

“Yayin da muke tunkarar zaben gwamna da na ’yan majalisar jiha, dole mu kara kokari domin shawo kan matsalolin da muka fuskanta a zaben da ya gabata.

“’Yan Najeriya ba za su yarda da wani abu ba bayan wannan.

“Dukkan ma’aikacin da aka samu da sakaci, ma’aikacin INEC ne ko kuma na wucin gadi ne, ciki harda masu tattara sakamako da turawan zabe, to ba za mu kyale su yi aikin zaben mai zuwa ba.

“Dole Kwamishinonin Zabe su dauki matakan da suka dace a wuraren da aka samu hujjojin cewa an yi abubuwa ba daidai ba,” in ji Farfesa Mahmood.