✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan filin jirgin saman London sun fara yajin aiki

Ma’aikatan filin jirgin saman Heathrow dake birnin London sun tsunduma wani yajin aikin sa’o’i 24 ranar Talata saboda yanke musu albashi.

Ma’aikatan filin jirgin saman Heathrow dake birnin London a a kasar Birtaniya sun tsunduma wani yajin aikin sa’o’i 24 ranar Talata saboda yanke musu albashi.

Tun da misalin karfe 11:00 na safe ne kimanin ma’aikatan filin 350 suka yi cincirindo a filin da nufin yin zaman dirshan har zuwa sa’o’i 24 masu zuwa.

Kazalika, wata mota za ta rika karakaina a filin jirgin dauke da mutum-mutumin Babban Jami’in filin jirgin, John Holland-Kaye da kuma wani zane mai dauke da rubutun “Filin jirgin Heathrow na zaftare albashin ma’aikata”.

Ana sa ran dai akalla ma’aikata 1,000 ne za su shiga yajin aikin da ya hada da ma’aikatan kwana-kwana, injiniyoyi, jami’an tsaro, masu kula da tashoshin filin da kuma masu kula da sauka da tashin jiragen.

Kungiyar ma’aikatan dai ta ce yunkurin da ake yi na zaftare wa mambobinta kusan Fan din Ingila kusan 8,000 ba abu ne da za ta lamunta ba.

Ma’aikatan za kuma su sake tsunduma wani yajin aikin a ranakun 14, 17 da 18 ga watan Disamba.

Filin jirgin saman Heathrow dai ya bayyana tafka asara mai dimbin yawa a bana saboda annobar COVID-19 wacce ta kai ta kusan Fan biliyan daya da rabi.