✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan Jami’ar FUAM na zanga-zanga kan albashin IPPIS

Sun bayyana tsarin biyan albashin IPPIS a matsayin wata hanyar cuta.

Ma’aikatan Jami’ar Harkar Noma ta Tarayya da ke Makurdi (FUAM), sun ki aminta da shiga tsarin IPPIS da gwamnatin tarayya ta fito da shi.

Ma’aikatan, karkashin jagorancin kungiyoyin NASU da SSANU, sun ce sun shiga zanga-zangar ce bayan umarni uwar kungiyar ta kasa.

Sannan sun ce gwamnati ta gaza cika alkawarin biyan mafi karancin albashin da aka yi a 2019.

Sannan kuma Gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawuran ta da daukar wa kungiyar tun shekarar 2012.

Ma’aikatan Jami’ar FUAM, Makurdi yayin zanga-zangar.

Ma’aikatan sun bayyana tsarin biyan albashi na IPPIS a matsayin wata hanyar cuta, saboda a cewarsu, tun bayan fito da tsarin suke fuskantar matsalolin biyan albashi da alawus-alawus dinsu.

Kwamared Moses Girgi, Shugaban NASU reshen jami’ar, ya ce tun bayan fito da tsarin IPPIS wasu kudadensu suka fara samun gibi.

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya, ta nemo mafita dangane da matsalar da tsarin albashi na IPPIS ya haifar a kasa baki daya.

Masu zanga-zangar dauke da kwalaye wanda ke dauke da rubutu kala-kala, sun yi wa kofar jami’ar tsinke tun a ranar Talata.

Sannan sun bukaci lallai gwamnatin ta martaba alkawarin da ta yi musu a 2019, na biyan su bashin da suke bi na albashi da alawus-alawus.