✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan jaridar Gaskiya 100 sun mutu suna jiran hakkokinsu

Sun shekara 15 suna jiran gwamnonin Arewa su biya su hakkokinsu

Mutum 100 daga cikin ma’aikatan kamfanin jaridar Arewa ta New Nigerian, masu wallafa jariar Gaskiya ta Fi Kwabo sun rasu a halin jiran a biya su hakkokinsu.

Shugaban hadaddiyar kungiyar ma’aikatan, Kwamaret Friday Idoko Ya ce tun shekarar 2012 suke jirar masu kamfanin kuma gwamnonin Arewa, su biya su albashin da suke bin su da suaran hakkokinsu, amma har yanzu babu labari.

Ya ce yawancinsu an tashe su daga gidajen haya, an koro ’ya’yansu daga makaranta saboda ba sa iya biyan kudade, baya ga wadanda suka rasu sakamakon fama da ciwon zuciya.

“Don haka muka taru, masu aiki da wadadna suka yi ritaya tun daga 2006 da muka yi wa gwamnonin Arewa aiki, mu bayyana muus takaicinmu kan tafiyar hawainiyar da suke yi wajen cefanar da kadarorin kamfanin kafin su biya mu hakkokinmu.

“A matsayinmu na shugabannin kungiyar, muna yin bakin kokarinmu wajen lallashin mambobinmu su kara hakuri, yayin da muke jiran gwamnonin su biya mu hakkokin,” inji shi.

A jawabinsa bayan babban taron kugiyar a Kaduna, Idoko ya jaddada kira ga gwamnonin 19 da su taimaka su biya su hakkokin nasu, ko za su samu saukin wasu abubuwan na rayuwa.

Idoko ya roki gwamnonin da su hanzarta sayar da kadarorin kamfanin su biya ma’aikatan, wadanda ya cikinsu har da wadanda suka yi ritaya, ke ta mutuwa ba tare da an biya su hakkokinsu ba.

Ya ce abin da suke bukata shi ne a ci gaba da aikin da aka faro na sayar da kadarorin kamfanin nan New Nigeria saboda yawancin kadarorin na zaune ne ba a amfani da su, wasunsu kuma ana yin kutse a cikinsu.