✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan kotu sun janye yajin aiki

Wata biyu suna yajin aikin kan kin ba bangaren shari'a ’yancin gudanar da kudi a jihohi.

Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta janye yajin aikin da ta shiga da ya dauki fiye da wata biyu.

Matakin janye yajin aikin ya biyo bayan taron shugabannin kungiyar JUSUN din da Hukumar Harkokin Shari’ah ta Kasa (NJC) wanda Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’ah Ibrahim Muhammad ya jagoranta.

Zaman ya amince da janye yajin aikin ne saboda maslahar kasa da kuma ba da damar aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla.

JUSUN ta fara yajin aikin ne tun ranar 6 ga watan Afrilu, 2021, domin nuna fushinta kan rashin bai wa bangaren shari’ar ’yancin cin gashin kai na kudadensa a jihohin kasar nan.