✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan lafiya sun gindaya sharadin janye yajin aiki

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya NMA reshen jihar Kuros Ribas, ta bayyana cewa ba za ta janye yajin aikin da ta shiga ba har sai…

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya NMA reshen jihar Kuros Ribas, ta bayyana cewa ba za ta janye yajin aikin da ta shiga ba har sai wani mambanta, Dokta Godwin Udo ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kuros Ribas Dokta Innocent Abang ne ya bayyana haka, yayin hirarsa da jaridar Punch a cikin wani shiri mai suna ‘Healthwise’ a ranar Juma’a.

Shugaban Kungiyar ya ce an yi garkuwa da likitoci hudu a jihar cikin shekarar nan, lamarin da ya sanya kwanaki hudu da suka gabata ta afka yajin aikin sai mama ta gani.

Dokta Abang ya ce “Abun ya zama ruwan dare, idan har rayuwarmu za ta zama cikin hadari, to ba mu da wani amfani ga al’umma don idan har rayuwar likita na cikin wani hali, ta ya zai taimaka wa mara lafiya.”

“Don haka babu yadda za a yi mu iya aiki cikin zulumi da dimuwa, shi ya sa mu yanke shawarar tsayar da komai har sai an saki abokin aikinmu,” inji Abang.

A ranar Larabar da ta gabata ce NMA (Nigerian Medical Association) reshen jihar Kuros Riba, ta shiga yajin aikin da ta ce ba za ta janye ba har sai ranar da aka saki abokin aikinsu sannan za su koma bakin aiki.

Shugaban kungiyar NMA, ya kara da cewa bai san dalilin da yasa masu garkuwa da mutane suka mayar da hankali a kansu ba.

A cewarsa “mambobin kungiyar mu hudu aka yi garkuwa da su a jihar cikin shekarar nan, wanda hakan ne ya tilasta muka shiga yajin aiki har sai ranar da aka saki abokin aikin namu.”

Daga bisani Dokta Abang ya yi addu’a da fatan dawowar Dokta Udo cikin koshin lafiya wanda baya bayan nan ya fada tarkon masu ta’adar garkuwa da mutane.